Yadda Rahama Sadau da ‘Yaruwarta suka taki sa’a, saura kiris harin jirgin kasa ya rutsa da su

Yadda Rahama Sadau da ‘Yaruwarta suka taki sa’a, saura kiris harin jirgin kasa ya rutsa da su

  • Rahama Sadau ta yi Allah-wadai da matsalar rashin tsaron da ake fama da shi a Arewacin Najeriya
  • ‘Yar wasan kwaikwayon ta ce saura kiris su bi jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a shekaran jiya
  • Sadau ta soki shugabannin da ake da su, ta yi kira ga mutane su shirya zaben mutanen kwarai a 2023

Kaduna - Fitacciyar ‘yar wasar kwaikwayon nan, Rahama Sadau ta yi magana a game da harin da ‘yan ta’adda suka kai a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja.

Rahama Sadau da ‘yanuwanta sun godewa Allah da ya kubutar da su daga wannan masifa. ‘Yar wasan fim din ta bayyana wannan ne a shafinta na Twitter.

Da ta ke magana a dandalin Twitter a ranar Talata, Sadau ta bayyana cewa da farko su na cikin wadanda suka yi niyyar bin jirgin kasan a yammacin Litinin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Ba a gama jimamin harin jirgin kasa ba, 'yan bindiga sun hallaka mutum 23 a Kaduna

Amma hakan bai yiwu ba, domin ba su yi dacen bin jirgin ba. A karshen wannan hani ya zama baiwa ga Rahman Sadau mai shekara 28 da wata ‘yaruwarta.

Sai dai duk da ta kubuta, tauraruwar ta bayyana cewa akwai mutanenta da su ka shiga jirgin ranar, kuma su na cikin wadanda ‘yan ta’addan suka kai wa hari.

Rahama Sadau da ‘Yaruwarta
Rahama Sadau da 'Yanuwanta Hoto: woman.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da Rahama Sadau ta ce a Twitter

“Ya kamata a ce ni kai na da ‘yar uwata mu na cikin wannan jirgi da aka kai wa hari a daren jiya (Litinin), amma sai ba mu samu bin jirgin ba.”
“Ba mu iya kama jirgin ba! Da har da mu, amma duk da haka dai mu abin ya shafa. Mu na da ‘yanuwa da abokai da suka shiga jirgin nan.”
‘Yaushe wannan abin zai zo karshe??? # KadunaTrainAttack.”(sic)"

Kara karanta wannan

Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

- Rahama Sadau, @Rahma_sadau

Sadau ta soki shugabannin Najeriya

Bayan nan kuma sai aka ji Sadau ta na sukar shugabanni, ta ba mutane shawara su tanadi katin zabe domin su tabbatar sun kada kuri’arsu ga wadanda suka dace.

“Abubuwa sai dai su kara muni yayin da zabe yake karasowa kuma Arewa ake kai wa hari. Sai in ce ku dauko katin PVC, ku zabi wadanda suka dace.”
“Amma kuma su wa za a zaba? Wadannan mutanen ne dai ake da su. Duk da haka, ku nemi PVC.”

- Rahama Sadau, @Rahma_sadau

A cewar Rahama Sadau, mutanen Arewa suka jawowa kan su wannan bala’i da ake fama da shi a yau, amma sun ki yarda shugabanninsu sun gaza tabuka komai.

Anyim ya tsaida kamfe

Dazu ne aka ji labari Sanata Anyim Pius Anyim ya fitar da jawabi ta bakin Ahmed Buhari, bayan samun labarin an kai hari ga jirgin kasan Kaduna-Abuja cikin dare.

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Anyim ya yi Allah-wadai da abin da ya auku, kuma ya ce ba zai fita yawon siyasa gaba daya makon nan ba. Anyim na cikin masu takarar shugaban kasa a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel