Harin jirgin kasa: Osinbajo ya soke tafiyarsa zuwa Lagas don taron ‘Birthday’ din Tinubu, ya ziyarci Kaduna

Harin jirgin kasa: Osinbajo ya soke tafiyarsa zuwa Lagas don taron ‘Birthday’ din Tinubu, ya ziyarci Kaduna

  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya isa Kaduna domin ganin irin barnar da yan ta’adda suka yi a jihar
  • Mahara sun farmaki wani jirgin kasa da ke hanyar zuwa Kaduna a daren ranar Litinin, 28 ga watan Maris daga Abuja
  • Mataimakin shugaban kasar na a hanyarsa ta zuwa wani taro a Lagas, kafin ya karkata akalar tafiyarsa zuwa jihar Kaduna

Kaduna - Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya isa jihar Kaduna, yan sa’o’i kadan bayan harin ta’addanci da aka kai kan jirgin kasa da ke dauke da fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna.

Kakakin mataimakin shugaban kasar, Laolu Akande, ya ce ubangidan nasa na a hanyarsa ta zuwa Lagas domin halartan taron ‘birthday’ din Tinubu amma sai ya karkata akalar tafiyar tasa zuwa Kaduna bayan ya samu labarin irin barnar da harin ya yi.

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Harin jirgin kasa: Osinbajo ya soke tafiyarsa zuwa Lagas don taron ‘Birthday’ din Tinubu, ya ziyarci Kaduna
Harin jirgin kasa: Osinbajo ya soke tafiyarsa zuwa Lagas don taron ‘Birthday’ din Tinubu, ya ziyarci Kaduna Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Laolu ya rubuta a shafinsa:

“A hanyarsa ta zuwa Lagas domin taron Tinubu na 13 domin bikin cikarsa shekaru 70 a duniya, Mataimakin shugaban kasar ya karkatar da tafiyarsa zuwa Kaduna da ranan nan bayan ya samu labarin irin asarar rai da dukiya da harin na jiya ya haddasa.”

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, shima ya tabbatar da tafiyar ta mataimakin shugaban kasar a wata wallafa da ya yi a shafinsa na twitter.

Ya rubuta cewa:

“VP Farfesa Osinbajo ya iso Kaduna da ranan nan domin samun bayanai daga tushe sannan ya yiwa mutane da gwamnatin jihar jaje kan harin bakin ciki na jiya da aka kai kan jirgin kasan Kaduna-Abuja.”

Gwamnatin jihar Kaduna ma ta sanar da zuwan nasa inda ta rubuta a shafinta cewa:

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wadanda suka jigata a harin jirgin Kaduna-Abuja

"Mallam Nasir @elrufai ya tarbi mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zuwa Kaduna. Mataimakin shugaban kasar ya isa asibitin sojoji na 44 don ganin wasu mutane da suka jikkata a harin jirgin kasan.”

Tinubu ya soke taron 'Birthday' dinsa don nuna jimamin harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

A gefe guda, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Ahmed Tinubu, ya soke taron da aka shirya domin bikin zagayowar ranar haihuwarsa karo na 70, jaridar The Guardian ta rahoto.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya bayyana hakan ne jim kadan bayan isarsa wajen taron a ranar Talata, 29 ga watan Maris.

Babban jagoran na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa ya ce taron ba zai iya ci gaba ba sakamakon wayar gari da aka yi an kai hari kan wani jirgin kasa da ke hanyar zuwa jihar Kaduna daga Abuja, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu ya soke taron 'Birthday' dinsa don nuna jimamin harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel