Yan takarar shugaban ƙasa uku a PDP sun haɗa sabuwar tafiya, sun shirya kwace mulki a 2023

Yan takarar shugaban ƙasa uku a PDP sun haɗa sabuwar tafiya, sun shirya kwace mulki a 2023

  • Yan takarar kujerar shugaban ƙasa uku karkashin inuwar PDP sun haɗa kan su, sun shirya yin sulhu domin kwace mulki a 2023
  • Jiga-Jigan siyasar uku sun ziyarci gwamna Ortom na jihar Benuwai domin neman goyon bayansa
  • A cewarsu, a shirye suke su sadaukar wa mutum ɗaya domin jam'iyyar PDP ta samu nasarar ceto Najeriya

Benue - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, da gwamna Bala Muhammed na Bauchi, sun ziyarci gwamnan Benuwai domin neman shawari game da takara.

Jiga-Jigan PDP ukun sun bayyana cewa sun dira jihar Benuwai kansu a haɗe domin tattaunawa da gwamna Samuel.Ortom, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Bukola Saraki, wanda ya yi jawabi a madadin tawagarsu, yace sun yanke hukuncin haɗa tawagar haɗin kai tsakanin su da nufin yin sulhu su fitar da mutum ɗaya a cikin su.

Kara karanta wannan

Bayan zabtare albashin masu mukamai, hotunan shugaban kasar Ghana a Aso Rock sun bayyana

Bala Muhammed, Bukola Saraki da kuma Aminu Tambuwal.
Yan takarar shugaban ƙasa uku a PDP sun haɗa sabuwar tafiya, sun shirya kwace mulki a 2023 Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Tsohon gwamnan jihar Kwara ya jaddada cewa sun zaɓi yin aiki a tawagar haɗin kai bisa ratsin kansu ba tare da wani ya tursasa su ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ƙara da cewa hakan da suka yi ya zama wajibi duba da yadda kawunan kasar nan suka rarrabu kashi daban-daban.

A kalamansa, Saraki ya ce:

"Yau gani anan tare da yan uwana, gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal da gwamnan Bauchi, Bala Muhammed. Mun zo nan ne a wani ɓangaren yawon neman goyon baya na mu uku da muka nuna sha'awar takara a PDP."
"Mu, a karan kanmu wasu yan makwanni da suka shuɗe, muka ji ya dace domin cigaban jam'iyya da kuma ƙasar mu, ya kamata mu haɗa kai mu yi sulhu. Burin mu ba komai bane idan aka haɗa da ƙasar mu."

Kara karanta wannan

Dan wasan Super Eagles, Shehu Abdullahi da jarumar Kannywood, Naja’atu, sun haifa yaro namiji

"Ina da kwarin guiwar zamu iya ceto Najeriya daga halin da ta shiga kuma a shirye muke mu sadaukar wajen fitar da mutum ɗaya, wanda zai haɗa kan mu, mu mara masa baya."

Wane matakai suka ɗauka don cimma nasara?

Saraki ya ƙara da cewa matukar suna son cimma nasara a abinda suka sanya a gaba dole ne su nemi haɗin kan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP.

"Dalilin zuwan mu nan kenan, mu uku kaɗai ba zamu iya kawo nasara ba, shiyasa muke jin mutane kamar ka (Ortom) wajibi ku shigo ciki."

Tsohon Sanatan ya kara da gode wa gwamna Ortom bisa tattaunawar da suka yi wacce ya kira da mai ɗaɗi kuma ta ƙare cikin nasara.

A wani labarin kuma Daga karshe, Ministan Buhari ya yi faɗi shirinsa kan takarar shugaban ƙasa a 2023

Ministan ayyuka da gidaje a Najeriya, Babatunde Fashola, ya ce babu takarar da zai fito a 2023 sai ta shugabancin gidansa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kashe babban Basarake a kan hanyar zuwa gaida mara lafiya

Ƙungiyoyi da dama sun jima suna kira ga Fashola ya shiga tseren shugaban kasa, amma ya ce matarsa da 'ya'yansa na can suna jiransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel