Harin Abuja-Kaduna: An gano yawan mutanen da yan bindiga suka kashe a harin jirgin ƙasa

Harin Abuja-Kaduna: An gano yawan mutanen da yan bindiga suka kashe a harin jirgin ƙasa

  • Wata majiya a kusa da tsahar jirgin ƙasa dake Rigasa Kaduna ta ce ana tsammanin fasinjoji Bakwai suka mutu a harin
  • Tuni dai hukumar sufurin jiragen ƙasa ta kasa ta dakatar da jigila a hanyar biyo bayan harin da yan ta'adda suka kai wa jirgin
  • Wani Fasinja da ya tsira ya bayyana cewa maharan sun zagaye Jirgin bayan sun ta da Bam, suka buɗe wa mutane wuta

Kaduna - Aƙalla mutum Bakwai ake fargabar sun rasa rayukan su a harin Bam da yan bindiga suka kai kan hanyar jirgin ƙasa ta Abuja-Kaduna jiya da daddare.

Wata majiya kusa da tashar jirgin dake Rigasa a Kaduna tace mutanen kuma fasinjojin jirgin sun mutu ne yayin harin, wasu kuma sun ɓata yayin da yan ta'adda suka tasa wasu.

Hafsan Sojojin Ƙasa ya ziyarci wurin da abun ya faru
Harin Abuja-Kaduna: An gano yawan mutanen da yan bindiga suka kashe a harin jirgin ƙasa Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hukumomin masu alaƙa da lamarin na kokarin haɗa kai da hukumar sufurin jiragen kasa ta ƙasa (NRC) domin gano bayanan Fasinjojin da abun ya shafa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Baya ga Azman, kamfanin jirgin Air Peace ya dakatar da aiki a Kaduna

Manajan hukumar NRC, Mista Fidet Okhiria, tun da farko ya tabbatar da kai harin ga manema labarai, kuma bai bada cikakken bayani ba.

Yadda lamarin ya faru

Wani Fasinja da ya tsira daga harin, ya gaya wa yan jarida ta wayar Salula cewa suna tsaka da tafiya, "Muka ji wata ƙara Buuuum, Bam ya tashi."

Ya kuma iya tuna wasu abubuwan da suka faru, inda ya ce:

"Ƙasa ta girgiza, yayin da idanuwa suka fara ganin giftawar harsasai, ƙarar bindiga ta mamaye wurin.

A cewarsa, Fasinjojin jirgin da suka kai kusan dubu ɗaya, sun faɗa kan juna yayin da taragon jirgin ya sauka daga kan hanya.

Ya ƙara da cewa yan ta'addan sun zagaye jirgin, sannan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, kuma mutane da dama sun jikkata sanadin haka.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: IGP da Shugaban Sojoji zasu je wurin da yan bindiga suka ɗana wa Jirgi Bam a Kaduna

A wani labarin kuma IGP da COAS Sun nufi wurin da yan bindiga suka ɗana wa Jirgi Bam a Kaduna

Shugaban yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, da shugaban Sojojin Najeriya, Janar Farouk Yahaya, zasu je wurin da yan bindiga suka dasa Bam.

Wannan na zuwa ne bayan wasu yan ta'adda sun dasa wa Jirgin ƙasa Bam, suka bude wa Fasinjoji wuta a layin Dogon Abuja-Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel