Harin filin jirgin saman Kaduna: 'Yan bindiga tserewa suka yi da ganin jami'anmu, gidan soja

Harin filin jirgin saman Kaduna: 'Yan bindiga tserewa suka yi da ganin jami'anmu, gidan soja

  • Rundunar soji ta yi martani a kan harin da yan bindiga suka kai filin jirgin saman Kaduna
  • Hukumar sojin ta ce a lokacin da maharan suka hango jami'ansu, tserewa suka yi
  • Ta jadadda cewar akwai cikakken tsaro a filin jirgin ta yadda yan bindigar ba za su iya kuskuren kai hari ba

Kaduna - Hukumar soji a ranar Litinin, 28 ga watan Maris, ta bayyana cewa yan bindiga basu isa su kai farmaki filin jirgin sama na Kaduna ba.

Da take martani kan kisan wani jami’in hukumar NAMA, rundunar tace lamarin ya faru ne kimanin kilomita shida dagatashar jirgin da kuma wajen katangar filin jirgin.

Da yake jawabi ga manema labarai a wajen harin, kwamandan rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Uriah Opuene, ya ce filin jirgin na Kaduna na da tsaro sosai.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka kwace iko a filin jirgin Kaduna daga harin da ‘yan ta’adda suka kai kan na’urori

Harin filin jirgin saman Kaduna: 'Yan bindiga tserewa suka yi da ganin jami'anmu, gidan soja
Harin filin jirgin saman Kaduna: 'Yan bindiga tserewa suka yi da ganin jami'anmu, gidan soja Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne lokacin da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, tare da kwamandan sansanin sojin sama, Air Commodore, Ademuyiwa Adedoyin, suka ziyarci wajen don gani da ido.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‎Kwamandan sojin ya ce akwai jami’an tsaro da dama a filin jirgin, kuma ‘yan bindiga ba za su iya kuskuran kai hari ba.

“Kamar yadda kuke gani, nan wajen yana da nisan kimanin kilomita shida ne daga filin jirgin saman.

Yan bindigar na wucewa ta bayan katangar filin jirgin ne kawai sai suka ga jami’in tsaron na NAMA sai suka bude masa wuta. Sai kawai suka yi amfani da wannan damar suka aika da wani sakon da yake ba daidai ba cewa sun kai hari filin jirgin.

Ya ce:

“Akwai matakan tsaro da yawa a filin jirgin; Wannan shi ne na farko kuma ko wannan na farkon ba a karya shi ba, domin tun lokacin da aka ji karar harbin, sai da mutanenmu suka dauki kusan mintuna uku kafin su iso nan daga na gaba.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Hana Jirgin Sama Tashi a Kaduna, Sun Bindige Mutum Daya Har Lahira

“Da isarsu, yan bindigar sun rigada sun fara guduwa, don haka muka fafata da su ta hanyar amfani da rundunar kasa. Sannan muka yi kira ga harin sama inda aka turo wani jirgi mai tashi da saukar ungulu kuma daga rahoton sama, kimanin yan bindigar 12 aka kashe.”

Har ila yau, kwamandan sansanin NAF ya ce an tsaurara matakan tsaro a yanikin filin jirgin saman gaba daya tun baya da aka yi kutse a makarantar horar da sojoji ta NDA a bara.

Ya kara da cewa ‘yan bindiga ba su da karfin kai hari a filin jirgin saman Kaduna.

Yadda sojoji suka kwace iko a filin jirgin Kaduna daga harin da ‘yan ta’adda suka kai kan na’urori

A baya mun ji cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne ‘yan ta’addan da yawansu ya kai 200 suka dire filin jirgin sama na Kaduna da ke karamar hukumar Igabi a Kaduna, inda suka dakile aiki tare da kashe jami’in tsaro daya na hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya.

Kara karanta wannan

An yankewa wacce ta raba man fetur a taro hukuncin watanni 27 a gidan yari

Harin ya haifar da tashin hankali a filin jirgin, inda rahotanni suka ce an hana jirgin AZMAN da ke kan hanyar Legas ya tashi da karfe 12:30 na rana.

Majiyoyi a hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya sun shaidawa jaridar Sunday Punch cewa, ‘yan ta’addan sun kai hari a wurin da kayan aikin VHF a filin jirgin suke kuma sun kashe wani jami’in tsaro da ke gadin wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel