Mulki ya samu: Bidiyo ya nuna sabon shugaban APC na buga wasan dara da wani sanata

Mulki ya samu: Bidiyo ya nuna sabon shugaban APC na buga wasan dara da wani sanata

  • Tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya taya Abdullahi Adamu murnar zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa
  • Sanata Kalu ya ji dadin wannan sabon mukamin na Adamu inda ya bayyana alfahari da cewa APC ta tabbata za ta samu nasara a 2023 tunda ta samu sabon shugaban jam’iyya
  • A wani bangare na sakon taya murna, tsohon gwamnan na Abia ya yada wani faifan bidiyo inda ya ke buga wasan dara tare da Adamu

Sanata Orji Uzor Kalu ya yada wani faifan bidiyo mai daukar hankali na kansa da sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, suna wasan dara.

Bidiyon dai na kunshe ne a sakon taya murna da majalisar dattawan ya aikewa Adamu kwana guda bayan hawa sabuwar kujerar mulkin APC bisa amincewar juna a taron gangamin APC na kasa da ya gudana.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC

Bidiyon wasa tsakanin Orji Kalu da shugaban APC Adamu
Mulki ya samu: Bidiyo ya nuna sabon shugaban APC na buga wasan dara da abokansa | Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Kalu wanda ya bayyana Adamu a matsayin cikakke kuma gogaggen dan siyasa ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa sabon shugaban na jam’iyyar APC zai nuna irin kwarewar da yake da ita wajen gudanar da harkokin tafiyar da gwamnati.

Sanatan ya ji dadin wannan ci gaba kuma ya bayyana cewa shugaban zai yi tasiri sosai a harkokin siyasa a matsayin shugaban jam'iyyar APC na kasa gogagge a aiki da sha'awa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa lallai Adamu yana da abin da ya kamata ya jagoranci jam’iyya mai mulki zuwa ga nasara a zaben 2023 mai zuwa.

A kalamansa:

“Na ji dadin fitowar tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
“Sabon shugaban zai yi amfani da gogewarsa ta siyasa da basirar gudanar da mulki wajen zaburar da goyon bayan talakawa ga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya karyata Gwamna Fayemi, ya fadi sirrin da Shugaban kasa ya fada masu

“Tsohon gwamnan dan Najeriya ne mai matukar kin nuna kabilanci, mai kishin kawo ci gaba da ci gaban kasa.
“Shugaban jam'iyya na kasa yana da abin da ya kamata jam’iyyar ta yi don ta yi nasara a zaben 2023 mai zuwa.

Minista sukutum da guda ya tare a birnin Abuja saboda tsabar 'tsoron' Gwamnan jiharsa

A wani labarin, tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi ya shaidawa Duniya cewa yana jin tsoron gwamna mai-mulki a halin yanzu a jiharsa Nyesom Wike.

Jaridar Daily Post a ranar Lahadi, 27 ga watan Maris 2022, ta rahoto Chibuike Rotimi Amaechi yana bayanin yadda dole ta sa ya tare a birnin tarayya Abuja.

Da ake hira da Chibuike Rotimi Amaechi a gidan talabijin, an yi masa tambaya kan taimakawa jam’iyyar APC ta karbe mulki daga hannun PDP a jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel