Bidiyon Wasu Matasa Suna 'Kaca-Kaca' Da Fuskar Tinubu a Hoto Ya Bazu a Dandalin Sada Zumunta

Bidiyon Wasu Matasa Suna 'Kaca-Kaca' Da Fuskar Tinubu a Hoto Ya Bazu a Dandalin Sada Zumunta

  • Wani bidiyo da ke nuna wasu matasa suna kaca-kaca da fuskar Ahmed Bola Tinubu a wani hoto ya bazu a dandalin sada zumunta
  • Ana kyautata tsamanin cewa an dauki bidiyon ne a lokacin da ake zanga-zangar neman kawo karshen rundunar yan sandan SARS a bara
  • Wasu matasan dai sun rika sukar tsohon gwamnan na jihar Legas ne domin suna masa kallon mai goyon bayan gwamnati da ke ci a yanzu ta APC

Wani bidiyo ya bayyana a dandalin sada zumunta. Bidiyon ya nuna wasu matasa suna zanga-zanga suna lalata fuskar Bola Ahmed Tinubu, jigon jam'iyyar APC na kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar.

Ana kyautata zaton an nadi bidiyon ne a lokacin zanga-zangar Endsars. A lokacin, jami'an tsaro sun bude wuta ga wasu yan Najeriya a Lekki Toll Gate.

Kara karanta wannan

Mu ya mu: ‘Yan takarar shugaban kasa na PDP sun gana don zaban daya kwakkwara

Bidiyon Wasu Matasa Suna 'Kaca-Kaca' Da Fuskar Tinubu a Hoto Ya Bazu a Dandalin Sada Zumunta
Bidiyon Wasu Matasa Suna 'Kaca-Kaca' Da Fuskar Tinubu a Hoto Ya Bayyana. Hoto: OJ.
Asali: Facebook

Tinubu, saboda matsayinsa na fitaccen mai goyon bayan gwamnati mai ci yanzu ya sha suka daga wurin masu zanga-zangar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga bidiyon a kasa:

A halin yanzu dai Tinubu na daya daga cikin wadanda ke kan gaba wurin neman gadon buzun Shugaba Muhammadu Buhari idan an yi zabe a 2023.

Tsohon gwamnan na Jihar Legas, tsawon shekaru da suka shude, ya kasance yana taka muhimmiyar rawa wurin nasarar shugabanni a kasar.

Tinubu ya gina dakin daukan karatu a LASU

A baya-bayan nan, ya bada gina cibyar shugabanci a jami'ar Legas, LASU, wanda kudinta ya kai Naira Biliyan 1.

Shugaban LASU, Farfesa Ibiyemi Olatunji Bello, ya sanar da bada kyautar dakin lakcan a LASU a ranar Alhamis.

Tinubu ya kuma yi kira ga gwamnati ta goyi bayan kamfanoni da za su samarwa matasa ayyukan yi domin su bada gudunmawarsu.

Kara karanta wannan

Ai ga irinta nan: Kalaman ‘Dan takarar Shugaban APC sun yi masa illa, an juya masa baya

2023: Ƙungiyar musulmai ta buƙaci Gwamna Ugwuanyi ya fito ya nemi kujerar Buhari

A wani rahoton, kungiyar hadin kan al’ummar musulmi, UMUL ta bukaci dan kabilar Ibo ya tsaya takarar shugaban kasa idan 2023 ta zo, The Sun ta ruwaito.

Kungiyar ta musulmai ta ce lokaci ya yi da cikin yankuna biyar da ke kasar nan, ko wanne yanki zai samu adalci da daidaito da juna, hakan yasa take goyon bayan Igbo ya amshi mulkin Najeriya.

Kamar yadda kungiyar ta shaida, dama akwai manyan yaruka uku a Najeriya, Hausa, Yoruba da Ibo, don haka in har ana son adalci, ya kamata a ba Ibo damar mulkar kasa don kwantar da tarzomar da ke tasowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel