Mu ya mu: ‘Yan takarar shugaban kasa na PDP sun gana don zaban daya kwakkwara

Mu ya mu: ‘Yan takarar shugaban kasa na PDP sun gana don zaban daya kwakkwara

  • Jiga-jigan 'yan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP sun gana da juna a shirinsu na zaban dan takara kwakkwara
  • Hakan na zuwa ne yayin da 'yan takara suka fara bayyana aniyarsu ta gaje kujerar shugaba Buhari a zaben 2023
  • Jam'iyyar PDP dai na ci gaba da hango kujerar Buhari, inda take ci gaba da shiri don ganin ta karbe kujerar

Abuja - A ranar Alhamis din da ta gabata ne ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP suka gana a Abuja, domin yanke shawari da ganin an samar da dan takarar daya kwakkwara gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa wannan na zuwa ne a matsayin ci gaba da gudanar da taron da aka fara a Bauchi.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Jiga-jigan sanatocin APC za su gana da shugaba Buhari a yau Alhamis

Jam'iyyar PDP kan batun tsayar da dan takara
Mu ya mu: ‘Yan takarar shugaban kasa na PDP sun gana don zaban daya kwakkwara | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki da gwamnonin jihohin Sokoto da Bauchi, Aminu Tambuwal da Bala Mohammed sun gana a Abuja kan lamarin.

Saraki, wanda ya yi wa ‘yan jarida jawabi a karshen taron, ya ce:

“Muna kasar nan a yau kuma yana da matukar muhimmanci a matsayin masu ruwa da tsaki a ga manyan shugabannin wannan jam’iyyar (PDP) sun hade kansu.
“Wasu daga cikin hukunce-hukuncen da muka kuma dauka a yau shi ne, za mu fara tuntubar sauran masu son tsayawa takara.
“Tabbas, an gano manyan shugabannin jam’iyyar da sauran masu son tsayawa takara a fadin kasar nan da kuma tsoffin abokan aikinsu; don haka za mu kai ga dukkan bangarorin kan wannan tsari na ganin mun tafi tare.
“Mun jajircewa kan wannan tsarin ne saboda mun yi imanin cewa da zarar mun hade a matsayin PDP, wadanda suka kafa ta tun tushe, don haka jam’iyya mai karfi za ta taimaka wajen kubutar da ‘yan Najeriya daga kalubalen da suke fuskanta a yanzu don ganin kasar ta kara karfi yayin da muke ci gaba.”

Kara karanta wannan

Ai ga irinta nan: Kalaman ‘Dan takarar Shugaban APC sun yi masa illa, an juya masa baya

Ba mu da shirin dakile 'yan takarar shugaban kasa, inji Saraki

Sai dai ya yi watsi da rade-radin da ake yi cewa taron nasu wani shiri ne na rufe bakin wasu masu 'yan takara ne daga samun tikitin jam’iyyar, yana mai cewa masu yada irin wadannan batutuwa basa ganin alheri.

Jaridar Guardian ta tattaro Saraki na cewa:

“Ba mu dakile kowa ba, kamar yadda muka ce, ba batun dakile kowa ba ne, a hada kan kowa da kowa ne domin maslahar kasar nan.
"Za ku ga lokacin da muka fara zagaye. Kamar yadda muka ce za mu gana da duk sauran masu neman tsayawa takara a jam’iyyar.”

Akwai matsala: PDP ta gargadi INEC kan sanya ido da halartar taron gangamin APC

A wani labarin, PDP ta gargadi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kada ta halarci taron gangamin jam’iyya mai mulki APC ko sanya ido kan lamurranta yayin tdaron.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

Legit.ng ta tattaro cewa jam’iyyar PDP ta yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da kakakinta Debo Ologunagba ya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris.

Jam'iyyar adawar ta bayyana taron na ranar Asabar 26 ga watan Maris a matsayin taron hauragiya da jam'iyyar mai mulki ta shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel