Ai ga irinta nan: Kalaman ‘Dan takarar Shugaban APC sun yi masa illa, an juya masa baya

Ai ga irinta nan: Kalaman ‘Dan takarar Shugaban APC sun yi masa illa, an juya masa baya

  • Wasu kusoshin jam’iyyar APC daga shiyyar kudancin Najeriya sam ba su tare da Abdullahi Adamu
  • Dalilin su kuwa shi ne Sanata Abdullahi Adamu yana cikin masu adawa da tsarin karba-karba a APC
  • Sanatan na kudancin jihar Nasarawa bai ganin dole ne mulki ya shiga hannun ‘Dan Kudu a 2023

Abuja - Yiwuwar Sanata Abdullahi Adamu na zama shugaban jam’iyyar APC na kasa ya na fusakantar barazana kamar yadda Nigerian Tribune ta rahoto.

Jaridar ta fitar da labari a ranar Laraba 23 ga watan Maris 2022 cewa wasu daga cikin ‘ya ‘yan APC ba su tare da shi saboda yana adawa da tsarin karba-karba.

Abdullahi Adamu yana cikin wadanda ba su ganin wajibi ne mulki ya komawa ‘Yan kudu 2023.

Kara karanta wannan

Lissafi ya canza: Shugaban kasa ya bada sabon umarni a kan zaben shugabannin jam’iyya

Wasu ‘yan APC sun yanke shawarar cewa ba za su goyi bayansa ba a wani taro da aka gudanar wanda mafi yawan gwamnonin jihohin kudu suka samu halarta.

An yi wannan taro ne ta kafar yanar gizo da nufin a samu hadin-kai a wajen zaben shugabanni. Hakan zai taimaka wajen samun hadin-kai a zaben da za a shirya.

Menene ra'ayin gwamnonin Kudu?

Wata majiya ta shaidawa jaridar duka gwamnonin face wani daya daga cikinsu, sun hadu a kan cewa bai dace a damkawa Sanata Adamu jagorancin jam’iyya ba.

APC South West
Wasu manyan APC a Kudu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Gwamnonin su na ganin tun da tsohon gwamnan na jihar Nasarawa bai goyon mutanen kudu su karbi shugabancin kasar nan a 2023, sam bai kamata a zabe shi ba.

Wani daga cikin masu zabe daga bangaren kudancin Najeriya ya ce ba su da wata matsala da Sanatan illa iyaka ya tabbatarwa Duniya cewa ya tsani shiyyarsu.

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: Gwamnonin APC sun gana da Shugaba Buhari a Abuja

Wannan mutumi ne da ya yi watsi da tsarin karba-karba, ya yi kaca-kaca da duk jagororin da ke goyon bayan haka, a cewar wani a cikin ‘ya ‘yan na jam’iyyar APC.

"Za mu yake shi a ranar zabe"

“Bai dace a yarda da wannan mutum ya jagoranci jam’iyyar da ta ratsa kasa irin APC ba. Za mu jira shi a ranar zabe, mu yake shi.”
“Ba za mu zabe shi ba saboda ya raina mutane, kuma bai ganin darajar ra’ayoyin wasu. Mun ji dadi da shugaban kasa ya ce bai tare da kowa.”
“An bar kowa ya shiga takarar, kuma a nan ne muke so mu yi masa sakayya, za mu ba shi (Abdullahi Adamu) mamaki.” Inji majiyar.

Menene matsayin Abdullahi Adamu?

Da aka yi wata hira da Sanatan na Nasarawa ta kudu kwanaki, ya nuna babu inda tsarin mulkin Najeriya ya ce a rika zagayawa da shugaban kasa ko wata kujera.

Kara karanta wannan

Idan PDP ta ba dan kudu tikitin shugaban kasa, ba zamuyi nasara ba: Tambuwal

Sanata Abdullahi Adamu ya na ganin babban burin masu kururuwar sai Najeriya ta watse, shi ne su zama magadan Muhammadu Buhari a zaben 2023, ba komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel