Caccakar Ganduje: 'Yan sandan Kano na neman Bashir Gentile ruwa a jallo kan sukar Ganduje

Caccakar Ganduje: 'Yan sandan Kano na neman Bashir Gentile ruwa a jallo kan sukar Ganduje

  • Rahotanni sun kawo cewa 'yan sanda a jihar Kano suna farautar hadimin Shekarau, Bashir Gentile
  • Ana neman shahararren mai sharhi kan harkokin siyasar ne kan zargin caccakar gwamnatin Abdullahi Ganduje
  • Majiyoyi sun zargi Ganduje da amfani da Bella Kano wajen saka Gentile a kwana

Kano - 'Yan sanda a Kano suna shirin kama shahararren mai sharhi a kan harkokin siyasa, Bashir Gentile, kan sukar gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje a shirin radiyo, Daily Nigerian ta rahoto.

Mista Gentile ya kasance hadimin tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau, sannan kuma hadimi ne ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

Caccakar Ganduje: 'Yan sandan Kano na neman Bashir Gentile ruwa a jallo kan sukar Ganduje
Caccakar Ganduje: 'Yan sandan Kano na neman Bashir Gentile ruwa a jallo kan sukar Ganduje Hoto: Daily Nigerian/BBC
Asali: UGC

A baya-bayan nan, masu sukar gwamnan da dama sun fuskanci hukunci, tsoratarwa daga yan sanda tare da gurfanar da su a gaban wasu alkalan jihar.

Kara karanta wannan

Maraba da Ramadan: Gwamnatin Ganduje ta yi gyara a Kalandar makarantun Kano saboda zuwan Azumi

Majiyoyi sun bayyana cewa bayan ba a samu nasara ba a yunkurin kama Mista Gentile, a yanzu yan sanda sun gayyace shi domin amsa tambayoyi kan wani korafi da aka shigar a kansa.

Majiyar ta ce hukumar yan sandan ta ce akwai wani korafi a kansa sannan cewa ana bukatar ganinsa domin magance lamarin.

A cewar majiyar, mai korafin shine Bella Kano, wani mai ba da shawara kan harkokin kudaden shiga da gwamnatin Kano ta dauka domin bunkasa kudaden shiga na jihar, rahoton Solacebase.

Majiyar ta ce:

“Kun ga Ganduje na amfani da Bella Kano wajen gasawa Gentile aya a hannu saboda sukar gwamnati mai ci a jihar da yake yi tsawon shekaru da dama.”

Da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa kan lamarin, kakakin yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce bai da masani a kan gayyatar ko shirin kama shi. Sai dai, ya ce zai zurfafa bincike kan al’amarin.

Kara karanta wannan

2023: Ina so na gaji Ganduje domin ci gaba daga inda ya tsaya, Sakataren gwamnatin Kano

'Yan sanda sun cafke tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano, Mu'azu Magaji a Abuja

A wani lamari makamancin haka, mun ji a baya cewa wasu jami'an rundunar yan sandan Najeriya, a birnin tarayya Abuja sun kama Mu'azu Magaji, tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano.

BBC Hausa ta rahoto cewa lauyansa da iyalansa sun tabbatar da kama tsohon kwamishinan a daren ranar Alhamis, inda suka ce an kama shi ne yayin da ya ke hanyar komawa masaukinsa.

Barista Garzali Datti Ahmad, lauyansa ya fada wa BBC Hausa cewa suna zargin akwai hannun gwamnatin Jihar Kano a kamen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel