Da Duminsa: 'Yan sanda sun cafke tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano, Mu'azu Magaji a Abuja

Da Duminsa: 'Yan sanda sun cafke tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano, Mu'azu Magaji a Abuja

  • Yan sanda sun kama Mu'azu Magaji, tsohon kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano a birnin tarayya Abuja
  • Iyalan Magaji da lauyansa sun tabbatar da kama shi a daren ranar Alhamis a lokacin yana hanyar komawa masaukinsa a Abuja
  • Garzali Datti Ahmad, lauyan tsohon kwamishinan ya ce yana zargin akwai hannun gwamnatin Kano a kamen duk da cewa kawo yanzu bata ce komai ba

FCT, Abuja - Wasu jami'an rundunar yan sandan Najeriya, a birnin tarayya Abuja sun kama Mu'azu Magaji, tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano.

BBC Hausa ta rahoto cewa lauyansa da iyalansa sun tabbatar da kama tsohon kwamishinan a daren ranar Alhamis, inda suka ce an kama shi ne yayin da ya ke hanyar komawa masaukinsa.

Da Duminsa: 'Yan sanda sun cafke tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano, Mu'azu Magaji a Abuja
Yan sanda a Abuja sun kama tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Zan sasanta da Ganduje amma bisa Sharaɗi ɗaya, Shekarau ya magantu

Barista Garzali Datti Ahmad, lauyansa ya fada wa BBC Hausa cewa suna zargin akwai hannun gwamnatin Jihar Kano a kamen.

Tsohon kwamishinan da aka fi sani da Dan Sarauniya, ya yi kaurin suna wurin sukar gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje da ta Shugaba Buhari tun kafin a sauke shi daga mukaminsa.

Har zuwa yanzu gwamnatin Jihar Kano ba ta yi magana game da kamen ba.

Ta yaya aka kama shi?

Barista Garzali ya ce 'yan sandan sun kama Mu'azu Magaji ne bayan bin motarsa a guje har suka jefa shi cikin kwatami.

Daga nan ne tsohon kwamishinan ya ja ya tsaya sannan yan sandan suka damke shi suka jefa shi a cikin motarsu suka yi awon gaba da shi.

Ya cigaba da cewa siyasa ce 'ta sanya aka turo yan sandan daga Jihar Kano domin su kama shi tunda bai aikata wani laifi a baya ba.'

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

Har wa yau lauyan ya ce za su bi kadin lamarin su kuma dauki matakin shari'a don ba za su bari wani da ke ganin ya kasaita ba ya taka doka a kyale shi.

Mu'azu ya dade yana sukar Gwamna Ganduje

Tun da dadewa, Mu'azu ya yi kaurin suna wurin sukar Gwamna Ganduje musamman bayan rikicin da ya saka Sanata Ibrahim Shekarau ballewa daga APC mai mulki a Kano ya kasa tsagin G-7.

A lokuta da dama ya rika sukar kamun ludayin gwamnatin Ganduje, wacce ya ce ba ta da alkibla.

Mu'azu ya rasa mukaminsa ne bayan wallafa wasu sakonni a Facebook da ake yi wa kallon na murna ne da rasuwar tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, da cutar korona ta yi ajalinsa.

Amma Mu'azu ya musanta hakan yana mai cewa ba murna ya yi ba da mutuwar Malam Kyari.

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

Kara karanta wannan

Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel