Maraba da Ramadan: Gwamnatin Ganduje ta umarce makarantu su ba ɗalibai hutu

Maraba da Ramadan: Gwamnatin Ganduje ta umarce makarantu su ba ɗalibai hutu

  • Yayin da Musulmai ke ta shirin tarban babban bako, gwamnatin Kano ta yi wani muhimmin gyara a Kalandar makarantun Firamare
  • Gwamnatin karkashin gwamna Ganduje ta ba da umarnin rufe Firamaren gwamnati da masu zaman kansu saboda Ramadan
  • Ta ce duba da falalar watan Azumi da kuma koken iyaye ne ya sa ta ɗauki wannan matakin

Kano - Gabanin ƙarisowar wata mai Alfarma na Ramadana, gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje, ta amince da gyara kalandar makarantu 2021/2022.

Daily Trust ta rahoto cewa gwmanatin Kano ta gudanar da gyara a Kalandar makarantun Firamaren gwamnati da masu zaman kan su a jihar saboda zuwan watan Azumi.

Gwamnan Kano, Dakta Ganduje
Maraba da Ramadan: Gwamnatin Ganduje ta umarce makarantu su ba ɗalibai hutu Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A cewar gwamnatin an rage mako ɗaya daga cikin mako 13 na zangon karatu na biyu, kuma an ƙara mako ɗaya a hutu, hakan zai sa ɗalibai su yi hutun mako 5.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro ta fatattaki Bayin Allah 700, 000 daga gidajensu a Zamfara inji Kwamishina

A wata sanarwa da kakakin ma'aikatar ilimi, Aliyu Yusuf, ya fitar, yace daidaita abun da gwamnati ta yi ya biyo bayan koken da iyaye suka gabatar na rokon a bar yara su yi azumi a gida.

Haka nan kuma ya bayyana cewa gwamnati ta ɗuba girma da Albarkar dake cikin watan Ramadana wajen amsa koken iyaye.

Bisa cimma wannan matasaya ne, ta umarci dukkan makarantun da abun ya shafa su tafi hutu daga 1 ga watan Afrilu, zuwa 8 ga watan Mayu.

Ku kula da ƴaƴanku saboda halin da ƙasa ke ciki - Kwamishina

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Muhammad Sanusi Sa’id, ya yi kira ga iyaye da masu kula su ƙara kokari wajen sanya ido kan yaransu saboda halin rashin tsaro da ƙasa ke ciki.

Kara karanta wannan

2023: Ina so na gaji Ganduje domin ci gaba daga inda ya tsaya, Sakataren gwamnatin Kano

Ya kuma roƙe su da su maida hankali wajen saka yayansu ayyukan da zasu amfane su, kamar Darasi a gida ko kuma kallon shirye-shiryen ilimi yayin wannan hutu.

Legit.ng Hausa ta tuntuɓi wani hedmasta na makarantar Firamare mai zaman kanta 'Aliya Nursery & Primary School' dake ƙaramar hukumar Ungoggo, Aminu Sulaiman Inuwa, ya shaida mana cewa:

"Mun samu labarin matakin da gwamnati ta ɗauka, kuma mu a karan kanmu Malamai mun ji daɗi domin ba karamin aiki bane haɗa koyarwa da Azumi a wannan yanayin."
"Azumin Ramadana lokaci ne da bawa ke bukatar komawa ga Allah ya ƙara yawan Ibada. A ɓangaren iyayen yara gaskiya ba su son hutu saboda hutu na sa yara su yi ta gararanba."
"Bansan ko wannan ba, amma idan zami hutu, iyaye ba su cika so ba, hankalinsu ya fi kwanciya su tura ƴaƴan su makaranta."

A wani labarin na daban kuma Allah ya karbi rayuwar ɗan kwamishinan Kwara awanni 24 bayan gama shagalin bikin ɗiyarsa

Kara karanta wannan

Karshen Mako: Yadda yan bindiga suka ɓarnata rayuka 62, sace wasu 62, suka kona gida 70 a Kaduna da Zamfara

Allah ya yi wa ɗan tsohon kwamishinan ilimi na jihar Kwara rasuwa awanni 24 bayan ya halarci bikin yar uwarsa a Ilorin

Tsohon kwamishina Musa Yeteti, ya nuna damuwarsa kan rashinsa, amma ya ce ya fawwala wa Allah komai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel