2023: Ina so na gaji Ganduje domin ci gaba daga inda ya tsaya, Sakataren gwamnatin Kano

2023: Ina so na gaji Ganduje domin ci gaba daga inda ya tsaya, Sakataren gwamnatin Kano

  • Gabannin zaben 2023, sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya ayyana kudirinsa na son takarar gwamnan jihar
  • Alhaji ya ce yana so ya hau kujerar domin ci gaba da kyakkyawan aikin gwamnatin Ganduje
  • Ya kuma sha alwashin aiki da gaskiya, amana da gudanar da harkokin jihar cike da tsoron Allah

Kano - Babban sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya ayyana aniyarsa ta son takarar kujerar gwamnan jihar a babban zaben 2023 mai zuwa.

Alhaji ya bayyana cewa yana so ya gaji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayinsa na wanda ake damawa da shi a gwamnatin, Daily Trust ta rahoto.

2023: Ina so na gaji Ganduje domin ci gaba daga inda ya tsaya, Sakataren gwamnatin Kano
2023: Ina so na gaji Ganduje domin ci gaba daga inda ya tsaya, Sakataren gwamnatin Kano Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Wazirin na Gaya ya sanar da kudirinsa ne a wani taron cin abincin dare da wata kungiya mai muradin shugabanci nagari ta gudanar a garin Kano a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

Sakataren gwamnatin ya kuma yi alkawarin nuna gaskiya, amana da gudanar da harkokin jihar cike da tsoron Allah.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alhaji ya ce:

“Ina da niyyar daurawa a kan kyawawan aikin Gwamna Ganduje domin gwamnatina ta samu karbuwa kamar yadda yake faruwa a jihohin Lagas, Kaduna da Borno.

Ya kara da cewa:

“Kun gani na kasance a wannan gwamnati tsawon shekaru 6. Kano na bukatar mutum mai gaskiya da rikon amana wanda zai iya ci gaba da kyakkyawan aikin gwamnatin Ganduje.”

Karshen PDP a Kano da Arewa kenan: Shugaban PDP ya damu da ficewar Kwankwaso

A wani labarin, da alamu dai ficewar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Kwankwaso daga PDP ka iya haifar da damuwa tsakanin 'ya'yan jam'iyyar PDP a jihar.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, Shehu Sagagi, ya ce barin Kwankwaso ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar NNPP babban kuskure ne.

Kara karanta wannan

Gawurtattun ‘Yan siyasa 12 da za su iya neman takarar Gwamnan jihar Kano a zaben 2023

Sagagi ya kuma yi kira ga manyan masu ruwa da tsaki na PDP da su tuntubi Kwankwaso domin jin matsalarsa da kuma neman hanyoyin magance su tun kafin lokaci ya kure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel