Karar kwana: Mako biyu bayan kwaso su, dalibin Ukraine ya mutu a jihar Sokoto

Karar kwana: Mako biyu bayan kwaso su, dalibin Ukraine ya mutu a jihar Sokoto

  • Wani dalibi dan asalin jihar Sokoto da ke karatu a kasar Ukraine Uzaifa Halilu Modachi, ya mutu
  • Modachi ya rasu ne a mahaifarsa mako biyu bayan kwaso su daga kasar sakamakon yakin Rasha da Ukraine
  • Marigayin ya shafe tsawon shekaru uku a can kasar ba tare da ya dawo gida hutu ba sai a bana da yaki ya barke

Sokoto - Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wani dalibi da ke karatu a kasar Ukraine, Uzaifa Halilu Modachi, ya mutu a jihar Sokoto, mako biyu bayan dawowarsa kasar.

Kafin mutuwarsa, an tattaro cewa Halilu Modachi ya shafe tsawon shekaru uku a kasar Ukraine ba tare da ya dawo gida hutu ba.

Karar kwana: Mako biyu bayan kwaso su, dalibin Ukraine ya mutu a jihar Sokoto
Karar kwana: Mako biyu bayan kwaso su, dalibin Ukraine ya mutu a jihar Sokoto Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Dalibin wanda yake shekararsa ta karshe a jami’ar koyon likitanci na Zaporozhye State Medical University Ukraine yana shirin zana jarrabawarsa ta karshe ne lokacin da yakin ya fara.

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

Naija News ta rahoto cewa Mahaifinsa, Hon. Habibu Haliru Modachi, dan majalisar dokokin jihar Sokoto ya fawwalawa Allah wannan ibtila’I da ya same shi inda ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Alhamdu Lilah, Allah ke bayar da rayuwa kuma shi ke daukar ta, kuma haka ya so ya faru, ko shakka babu kan haka.
“Da ace a kasar Ukraine ya rasu da an fadi abubuwa da dama game da shi, cewa imma harin Rasha ne ya kashe shi ko kuma ya yi hatsari koma ace sojojin Ukraine ne suka harbe shi bisa kuskure.
“Mun godewa Allah da yam utu a gabanmu, mun kuma gode wa gwamnatin Najeriya musamman ta jihar Sokoto da ta dauki matakin gaggawa don kwashe su kafin yakin ya ta’azzara a Ukraine.”

Ka kawo mana dauki, ana kai mana hari: Daliban Najeriya dake Ukraine ga Buhari

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jirgin sama ya yi hadar da mutane 133 a China, da dama sun mutu

A gefe guda, mun kawo a baya cewa kungiyar daiban Najeriya dake karatu a kasar Ukraniya sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari yayi gaggawan kwashesu daga kasar.

Wannan ya biyo bayan yakin da ya barke tsakanin kasar Rasha da Ukraniya kuma kimanin mutum 50 sun mutu.

A wasikar mai taken, "BUKATA NA GAGGAWA GA SHUGABAN NAJERIYA MUHAMMADU BUHARI" da kungiyar ta aike ranar Alhamis, daliban sun bayyana yankunan da akwai yan Najeriya da aka kaiwa hari, rahoton DailyTrust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel