Da Duminsa: Jirgin sama ya yi hadari da mutane 133 a China, da dama sun mutu

Da Duminsa: Jirgin sama ya yi hadari da mutane 133 a China, da dama sun mutu

  • Labari daga kasar waje ya ayyana cewa, wani jirgin sama ya fadi a kasar China, yana dauke da mutane sama da 100
  • Jirgin an ce ya fadi ne a wasu yankunan kasar kuma ana fargabar mutane da dama sun mutu, wasu sun jikkata
  • Ya zuwa yanzu, ba a san adadin mutane da suka mutu ba, kana ba a san adadin wadanda suka jikkata a hadarin ba

China - Wani jirgin saman fasinja na Gabashin China dauke da mutane 133 ya yi hatsari a Kudu maso Yammacin kasar China wanda ba a san adadin wadanda suka mutu ba.

Kafar labarai ta TRT ta rahoto daga gidan talabijin na CCTV cewa:

"Jirgin saman Boeing 737 na kasar China mai lamba 737 dauke da mutane 133 ya yi hadari ne a gundumar Teng da Wuzhou da Guangxi, kuma ya haddasa gobara a tsaunuka."

Kara karanta wannan

Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna Obinao garin tserewa Amurka

Jirgi ya fadi a kasar China
Da duminsa: Jirgin sama dauke da mutane 133 ya yi hadari a China, da dama sun mutu | Hoto: Daga bidiyon da kafar labaran kasar China ta yada aka yanke shi, inji hindustantimes.com
Asali: UGC

Rahoton ya kara da cewa an aike da tawagogin agajin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya afku, kuma kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani kan adadin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikkata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafofin yada labarai na China sun ruwaito cewa jirgin bai isa birnin Guangzhou ba, bayan da ya taso daga birnin Kunming jim kadan bayan karfe 0500 agogon GMT (1:00 na rana) a ranar Litinin, kamar yadda ma'aikatan filin jirgin suka ruwaito.

Hindustan Times ta tattaro cewa, jirgin ya daina musayar bayanai a Kudu maso Yammacin birnin Wuzhou na kasar China.

A tarihin jirgin, an kai shi zuwa Gabashin kasar ne daga Boeing a watan Yunin 2015 kuma ya kwashe sama da shekaru shida yana shawagi a kasar.

Bidiyo ya nuna hayaki a wurin da jirgin ya fadi

Kara karanta wannan

Yan Boko Haram sun sace Likita daya tilo dake asibitin Gubio, jihar Borno

Jaridar Insider Paper ta yada wani bidiyon da tace na jirgin ne lokacin da yake ci da wuta.

Legit.ng Hausa ta duba bidiyon, ta yadda hayaki ke tashi daga nesa, lamarin da ke nuna akwai alamar afkuwar gobara bayan fadowar jirgin.

Wani jirgin sama da ya dauko 'yan sanda ya yi hatsari a Bauchi

A wani labarin, gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa, wani jirgin sama mai saukar ungulu na ‘yan sanda da ya taso daga Abuja ya yi hatsari a filin tashi da saukar jiragen sama na Bauchi, Hukumar Binciken Hatsari ta bayyana a ranar Alhamis.

Sai dai, ba a sami asarar rai ba, in ji rahoton na AIB.

A cewar sanarwar da The Nation tace ta samo:

“A ranar 26 ga Janairu, 2022, Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (NAMA) ta sanar da Ofishin Binciken Hatsarin Hatsari, Najeriya game da wani hatsarin da ya rutsa da wani jirgin sama mai lamba Bell 429 mai lamba 5N-MDA mallakin rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF). "

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Bindige Jigon Jam'iyyar PDP, An Garzaya Da Shi Asibiti

Asali: Legit.ng

Online view pixel