CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

  • Kungiyar CAN ta yiwa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai wankin babban bargo a kan rashin tsaro
  • Shugaban kungiyar reshen Kaduna, Reverend John Joseph Hayab, ya bukaci El-Rufai da ya ajiye girman kai sannan ya yarda cewa ya gaza a wannan fannin
  • Hayab ya kuma bukaci jama'a da su nemi hanyar kare kansu daga yan bindiga tunda gwamnati ta gaza basu kariya

Kaduna - Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta yi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya ajiye girman kai sannan ya yarda cewa ya gaza magance kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ta’addanci da ke gudana a jihar, Daily Trust ta rahoto.

Shugaban CAN reshen jihar Kaduna, Reverend John Joseph Hayab, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, inda ya fadama El-Rufai da tawagarsa da su mayar da hankali kan yakin da ceto jihar domin a tuna da shi a alkhairi bayan ya bar mulki.

Kara karanta wannan

2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki bisa saboda sha'awar kujerar gwamna

Jawabin CAN na zuwa ne a daidai lokacin da aka karya doka da oda a yankin kudancin jihar.

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro
CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro Hoto: The guardian
Asali: UGC

Hayab ya ce abun damuwa ne yadda ake ci gaba da kashe-kashe, garkuwa da mutane da fashi da makami a jihar ba tare da daukar wani kwakkwaran mataki ba daga gwamnati da hukumomin tsaro.

Vanguard ta kuma rahoto cewa Hayab ya bukaci wadanda abun ya shafa da su nemi hanyar kare kansu daga yan bindiga.

Ya ce:

“Har zuwa wani lokaci wannan mummunan lamari zai ci gabakuma shin shugabanninmu za su yi abun da ya kamata? Al’umman jihar Kaduna sun gaji da martanin gwamnati ba tare da wani kwakkwaran mataki don kare rayuka da dukiyoyi ba.
“Saboda haka, muna so mu ji sannan mu ga masu kashe mutane da masu garkuwa da mutanen da aka kama saboda Allah wadai da gwamnati ta saba yi a kafafen yada labarai a duk lokacin da aka yi barna bai wadatar ba.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

“A halin yanzu, muna rokon al’umma da su farka sannan su yi abun da ya kamata, su kare rayukansu da garuruwansu. Idan gwamnati ta gaza kare ka, sai kai ka nemi hanyar kare kanka.
“Kamar yadda yake a bayanai, jihar Kaduna ta rasa rayuka da yawa a cikin shekaru hudu da suka gabata yayin da da kyar shugabanni ke nuna tausayawa ko damuwa ga mutanen da abun ya ritsa da su duba ga cewar martanin gwamnati ya kan zo ne a kafofin watsa labarai. Abun bakin ciki, wadanda aka kashe ba sa iya karatu ko sauraron labarai.
“Saboda haka wani amfani Allah wadai na kafar watsa labarai ke yi? CAN na kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta hadiye girman kanta sannan ta yarda cewa ta gazawa mutane, ta nemi taimako domin gaggauta magance kashe-kashe, garkuwa da mutane da ayyukan ta’addanci da ke gudana a jihar.
“Ya kamata gwamna El-Rufai da tawagarsa su mayar da hankali a kan yakin domin ceto jihar don a tuna da shi na alkhairi idan ya bar kujerar mulki.”

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hadarin mota ya lakume mutane 11 a hanyar Zaria zuwa Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana fita a yankuna 3 na jihar

A wani labarin, gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita hana fita a kananan hukumomin Jema’a da Kaura biyo bayan samun bayanai na shawari daga hukumomin tsaro na jihar.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta shafinta na Twitter.

Sanarwar ta ce: "Biyo bayan shawarwarin hukumomin tsaro, KDSG ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura tare da fara aiki nan take. Hakan na nufin taimakawa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura a yankunan, da ceton rayuka da dukiyoyi da kuma ba da damar maido da doka da oda."

Asali: Legit.ng

Online view pixel