Da duminsa: Ka kawo mana dauki, ana kai mana hari: Daliban Najeriya dake Ukraine ga Buhari

Da duminsa: Ka kawo mana dauki, ana kai mana hari: Daliban Najeriya dake Ukraine ga Buhari

  • Daliban Najeriya mazauna kasar Ukraniya sun kai kuka ga shugaba Buhari ya kwashesu cikin gaggawa
  • Daliban sun aika wasikar kar ka kwana ga Buhari saboda an fara kai musu hare-hare a wuraren zamansu
  • Gwamnatin tarayya da majalsar wakilai tuni sun yi alkawarin kwaso daliban

Kungiyar daiban Najeriya dake karatu a kasar Ukraniya sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari yayi gaggawan kwashesu daga kasar.

Wannan ya biyo bayan yakin da ya barke tsakanin kasar Rasha da Ukraniya kuma kimanin mutum 50 sun mutu.

Ukraine ga Buhari
Da duminsa: Ka kawo mana dauki, ana kai mana hari: Daliban Najeriya dake Ukraine ga Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wasikar mai taken, "BUKATA NA GAGGAWA GA SHUGABAN NAJERIYA MUHAMMADU BUHARI" da kungiyar ta aike ranar Alhamis, daliban sun bayyana yankunan da akwai yan Najeriya da aka kaiwa hari, rahoton DailyTrust.

Kara karanta wannan

Duk wanda yayi mana shisshigi kan yakinmu da Ukraniya zai fuskanci ukuba, Shugaban kasan Rasha

Shugabar NANS dake Ukraniya, Eunice Eleaka, ta rattafu hannu, kan wasikar.

Wani sashen jawabin yace:

"Muna aike wannan wasika ne bisa rikicin Rasha da Ukraniya wanda yayi muni da safiyar nan 24 ga Febrairu 2022 inda aka fara tashin bama-bamai da harbe-harbe a wuraren da yan Najeriya ke zama."
"Muna rokonka mai girma Shugaba MUHAMMADU BUHARI ka aiko a kwashe daliban Najeriya dake Ukraniya."

Gwamnatin tarayya zata kwaso yan Najeriya dake zaune a kasar Ukraniya

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin da take y na kwashe yan Najeriya dake zaune a Ukraniya sakamakon yakin da ya barke tsakanin kasar da Rasha a ranar Alhamis.

Gwamnati ta ce tana shirya jirgi na musamman da don kwaso su muddin aka bude tashohin jirgi.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, a hirar da yayi a tashar NTA yace an tuntubi ofishin jakadancin Najeriya dake Kiev kan shirya yadda za'a kwaso wadanda ke niyyar dawowa gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel