'Karin bayani: Bayan watsi da kujerar da Ganduje ya bashi, Yakasai ya fita daga APC

'Karin bayani: Bayan watsi da kujerar da Ganduje ya bashi, Yakasai ya fita daga APC

  • Tsohon hadimin gwamnan jihar Kano ya fitar da fitarsa a jam'iyyar APC, inda yace sam yanzu ba shi babu ita
  • Ya bayyana haka ne tare da zayyano dalilansa da yake ganin bai kamata jam'iyyar APC ta kasance a haka ba
  • Ya bayyana abubuwa da dama da suka faru kafin kafuwar APC, da kuma yadda abubuwa ke tafiya a yanzu

Tsohon mai taimakawa gwamnan jihar Kano kan harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakasai ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki.

Yakassai ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Instagram a ranar Litinin, 21 ga Maris.

Ya bayyana cewa dalilinsa na ficewa daga APC shi ne saboda gazawarta wajen ci gaba da kiyaye alkawuran da ta yi wa jama’a a lokacin yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka yiwa dan majalisar Neja ruwan duwatsu da ihun 'Ba ma yi' bayan ya ziyarci mazabarsa

Yakasai ya bayyana yadda ya sha fama wajen tallata jam'iyyar APC a kasar domin ganin ta kafa gwamnatin da za ta kawo sauyi ga miliyoyin 'yan Najeriya gabanin zaben 2015.

A wani rubutu da ya yada a shafinsa na Facebook, Legit.ng Hausa ta gano inda yake cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina cikin wadanda suka zaga kasar nan domin yin tallan jam'iyar ta APC sanda aka kafa ta, tun daga matakin mazabu, zuwa jiha da kasa baki daya. Na sadaukar da rayuwa ta tare da mika wuya na kacokan, wajen gina jam'iyyar, da zummar cewa zamu kawo sabon sauyi a kasar nan, tare da fiddo da miliyoyin yan Najeriya daga cikin mawuyacin halin da muke ciki, na kuncin rayuwa, da samar da yalwatar arziki da aikin yi da tsaro da sauran su."

Hakazalika, ya bayyana cewa, yana daga cikin wadanda suka yayata APC gabanin zaben 2019, amma gashi har yanzu kasar na fama da wahalhalu daban-daban.

Kara karanta wannan

Budurwa ta yi watsi da saurayin da ya kashe N1m don tafiyarta UK, ya fada tashin hankali

A cewarsa:

“A shekarar 2019, haka muka sake fita neman kuri'a ganin cewa watakila shekaru hudu sunyi kadan a iya wani abin kirki ganin yadda al'amuran suka lalace matuka, dan haka muka sake neman mutane su zabi gwamnatin mu ta APC, wanda aka lashe zaben a karo na biyu. Sai dai abin takaicin shine a zaben farko da na biyun, duk kwalliya bata biya kudin sabulu ba, da gwamnatin da jam'iyar duk sake tabarbarewa al'amuran su, su kayi."

A cikin dogon rubutun, ya bayyana dalilansa na dawowa daga rakiyar jam'iyyar APC, inda ya mika godiya ga mutane da dama, ciki har da mai gidansa a baya; Gwamna Ganduje.

Ya kara da yin tsokaci kan irin halin da ya shiga a shekarar 2020 inda ya sha wulakanci daga hannun gwamna mai ci kan yadda ya fadi gaskiya kan gazawar jam’iyyar ta APC wajeN tafiyar da mulki.

Karanta cikakken bayanin da ya yi kan ficewarsa a APC:

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Tashin hankali yayin da jiga-jigan PDP 70 suka sauya sheka zuwa APC

A wani labarin, jaridar Leadership ta rahoto cewa, jam’iyyar APC reshen jihar Gombe ta samu karbuwa yayin da ta karbi wasu mutane 70 da suka sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP a karamar hukumar Dukku da ke jihar.

Jiga-jigan wadanda shugabannin jam’iyyar a unguwannin a karamar hukumar ne sun bayyana sauya sheka zuwa APC a karshen mako a lokacin da suka ziyarci gwamnan jihar, Inuwa Yahaya.

Da yake karbarsu, gwamnan wanda shugaban ma’aikatan sa Abubakar Kari ya wakilta ya bayyana jin dadinsu da sauya shekarsu zuwa jam’iyya mai mulki tare da ba su tabbacin cewa za a dauke su tamkar tsofaffin ‘ya’yan jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel