Budurwa ta yi watsi da saurayin da ya kashe N1m don tafiyarta UK, ya fada tashin hankali

Budurwa ta yi watsi da saurayin da ya kashe N1m don tafiyarta UK, ya fada tashin hankali

  • Wani mutumi dan Najeriya ya shiga damuwa bayan budurwarshi ta yaudareshi, bayan ta tare a kasar waje
  • Mutumin ya kashe kusan N1 miliyan wajen daukar nauyin budurwar zuwa Ingila don cikar burinta
  • Matar ma'aikaciyar lafiyar ta yanke shawarar yanke alakar, ta hanyar nuna mishi bukatar rabuwa da ita, don ta maida hankali kan aikin ta

Wani dan Najeriya ya shiga damuwa bayan kashe kusan N1 miliyan don daukar nauyin budurwarsa zuwa ingila, inda daga bisani tayi watsi dashi gami da yin zaman dirshan a kasar waje.

@akunesiobike 12 ne ya wallafa labarin a Twitter, gami da bayyana yadda lamarin ya auku da abokinshi wanda ke zaune a Ingila.

Budurwa ta yi watsi da saurayin da ya kashe N1m don tafiyarta UK, ya fada tashin hankali
Budurwa ta yi watsi da saurayin da ya kashe N1m don tafiyarta UK, ya fada tashin hankali. Hoto daga Kirsty O'Connor, Europa Press
Asali: Getty Images

Abokin nashi ne ya taimakawa budurwar wajen cika burinta. Kamar yadda mai amfani da kafar sada zumuntar Twitter ya bayyana, abokin nashi ya bawa budurwar kudi don zana jarabawar IELTS, CBT saboda ta cika burinta na komawa Ingila dindindin.

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Bayan komawarta Ingila, budurwar ta ce ko kadan bata ga mijin aure a tare dashi ba, kuma tana bukatar mayar da hankali kan aikinta, sannan ta na so ya rabu da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalaman da ta fada mishi sun tarwatsa shi, yayin da mutumin ya tuko zuwa gurin ta don su yi magana gaba-da- gaba, amma sai ta nuna mishi halin ko in kula.

"A lokacin da mutumin nawa ya dauki awanni hudu yana tuki zuwa gidanta, bata iya bashi kofin ruwa ko wani abu da zai ci ba. Tun lokacin zuciyar sa ta karye. Gaskiya na tausaya mai."

Mutumin ya gane tsohuwar buduruwar tasa ta samu wani daban.

"Babban abun takaici shi ne yadda gayen ya dauka tsawon awanni hudu yana tuki zuwa gidanta, amma wani mutumi dan Najeriya yazo ya dauke ta, a gaban abokin nawa. Ji nayi kamar in fashe da kuka a lokacin da ya bani labarin," mai amfani da kafar sada zumuntar Twitter ya wallafa.

Kara karanta wannan

A bidiyo mai taba zuciya, angon amaryar da aka birne ranar bikinsu yace ta ji a jikinta mutuwa za ta yi

Jamara sun yi martani

Babu bata lokacin matasa suka fara tsokaci kan wallafa, ga wasu daga cikin martanin jama'a:

@Mirabel_098 ta ce: "Wannan labarin ba zai hana mutane kai masoyansu kasashen katere ba, saboda wasu mutanen da ba na kwarai ba, wadanda basu cancanci so da kulawa ba, ba yana nufin kowacce budurwa ko saurayi zai yi hakan ba, kawai mu yi fatan haduwa da na kwarai don gudun asarar da lokacin mu wurin gina mutanen banza."
@Ayo_bami007 ya ce: "Ya san da cewa yarinyar bazata ta taba sonsa ba, shiyasa ya yanke shawarar dage wa akan kyautata ma ta, da sa ran za ta canza ra'ayinta a kan sa. Sai dai, ba za ka tilasta wa mutum ya soka ba.
"Na tausayawa abokinka yadda ya siyar da kan shi da arha."
@chyagsx ya ce: "Kanwata za ta zo Ingila, saurayinta ne zai dau dawainiyar komi. Sai dai yayi ta rokon kanwata ta koyi tuki kamar yadda ya dage, amma taki. Yanzu 'yar uwar tawa na tuka mota. Ba zata iya zuwa Ingila tayi shirme ba."

Kara karanta wannan

Budurwa ta danna wa saurayinta wuka har lahira kan kyautar N3,000 da zasu raba

@IntangibleUmoh ya ce: "Na san wani abokina da ya dawo Najeriya daga Canada don ya auri budurwarsa. Bayan sun haifi dansu na fari, ya nema ma ta mazaunin dindindin. Ita kuma ta rabu da shi a filin jirgi a lokacin da suka isa Toronto. Haka auren ya rabu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel