Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

  • Dan takarar shugaban shugaban kasa a Najeriya, Dele Momodu ya bayyana bukatar tallafi daga mabiyansa
  • Dele Momodu ya bayyana cewa, akwai bukatar masoyansa su biya kudade domin daukar nauyin takararsa
  • Ya bayyana haka ne a Twitter, inda ya ajiye lambobin asusun banki domin zuba masa kudi komin kankantarsu

A cikin mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya, fitaccen dan jarida Dele Momodu, ya tunkari ‘yan Najeriya, da sauran masu bibiyar kafafen sada zumunta na duniya da su mara masa baya wajen neman kujerar shugaban kasa.

Ya nemi gudunmawarsu ne domin cimma burinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa, Punch ta ruwaito.

Dele Momodu na neman taimakon jama'a
Ku tara min kudin kamfen: Dan takarar shugaban kasa ya roki 'yan soshiyal midiya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wannan matakin, in ji shi, zai taimaka masa da sauran masu neman dawo da martabar Najeriya, da kuma tabbatar da an dora kasar a kan turbar ci gaba da kuma saurin habaka kasar.

Kara karanta wannan

2023: Wani Ɗan Kasuwa Mazaunin Abuja Ya Shiga Jerin Masu Neman Gadon Kujerar Buhari a APC

Momodu wanda shi ne mawallafin Mujallar Ovation, ya yi wannan roko ne a ranar Laraba ta hanyar wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Momodu ya kuma saki wasu asusu na banki da suka hada da na dala da Yuro da fam da naira domin bayar da gudunmawar, yayin da ya bukaci mabiyansa da cewa ba zai raina kyauta ba.

PDP ta tausayawa matasa wajen biyan kudin fam din takara, ta rage masu 50% da wasu hukunci 11 da ta zartar

A wani labarin, a wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakaten PDP, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa dukka matasa da ke tsakanin shekaru 25 da 30 wadanda ke shirin neman takarar mukamai daban-daban za su biya kaso 50 cikin dari na kudin fam din takara.

Ologunagba a cikin wani jawabi da Legit.ng ta gano, ya bayyana cewa jam’iyyar ta yanke hukuncin ne a wata sanarwa cikin wata sanarwar da ta fitar a karshen taron kwamitin zartarwar PDP karo na 95.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Ɗiyar Bola Tinubu ta yi tsokaci kan shirin mahaifinta na gaje kujerar Buhari

A cewar Ologunagba, an gudanar da taron NEC din ne a sakatariyar jam’iyyar na kasa a Wadata Plaza da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel