Babban Magana: 'Yan Sanda Sun Cafke 'Aljani' Da Ya Yi Yunƙurin Yin Damfarar N2.2m a Borno

Babban Magana: 'Yan Sanda Sun Cafke 'Aljani' Da Ya Yi Yunƙurin Yin Damfarar N2.2m a Borno

  • Rundunar yan sanda a jihar Borno ta yi nasarar damke wani da damfarar mutane da sunan 'aljani' kuma zai iya azirta su da dukiya mai yawa.
  • An kama wanda ake zargin ne bayan damfara wani mutum har Naira miliyan 2.2 a Borno amma kuma bai yi arzikin ba sai dai talaucewa
  • Kwamishinan yan sandan Borno, Abdu Umar, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ana binciko wadanda ya ke aiki tare da su

Borno - Rundunar yan sanda a Jihar Borno ta kama wani da ake zargin ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar karyar cewa shi aljani ne kuma yana iya azurta su da kudi.

Kwamishinan yan sandan jihar Borno, Abdu Umar, ya shaida wa manema labarai a Maiduguri a ranar Juma'a cewa asirin wanda ake zargin ya tonu, mamba na tawagar wasu su uku, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Putin ya tsure, ya tattara ma’aikata 1000 ya kora saboda tsoron a sa masa guba a Rasha

Babban Magana: 'Yan Sanda Sun Kama 'Aljani' Da Ya Yi Yunkurin Yin Damfarar N2.2m a Borno
'Yan Sanda Sun Kama 'Aljani' Da Ya Yi Yunkurin Yin Damfarar N2.2m a Borno. Hoto: Vanguard Nigeria
Asali: Twitter

Umar ya ce dabarar da wadanda ake zargin suke yi shine suna yaudarar wadanda suke cuta cewar suna harka da aljanu ko rufanai wanda za su iya azurta su da kudi mai yawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce wanda ake zargin, da abokan harkallarsa da a yanzu ana nemansu, sun tuntubi wani Bukar Mohammed suka yaudare shi cewa za su iya tamaka masa ya yi kudi.

"Sun masa dabara suka umurci shi ya tafi wani wuri ya ajiye katinsa na cire kudi a banki wato ATM da lambar sirrinsa a wurin.
"Wanda abin ya faru da shi ya aikata hakan kuma wadanda ake zargin suka cire kudi Naira miliyan 2.2 daga asusun bakinsa," a cewar Umar.

Kwamishinan yan sandan, kamar yadda Vanguard ta rahoto ya ce a yayin bincike, an binciko wanda ake zargin aka kuma kama shi a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Kamfanonin sadarwa su na maganar kara farashin yin wayar salula saboda tsadar mai

Wanda ake zargi ya amsa laifisa, In ji CP Umar

Ya kara da cewa daga bisani wanda ake zargin ya amsa laifinsa da wasu laifuka masu alaka da damfarar.

Umar ya ce ana nan ana kokarin kamo sauran abokan harkallarsa domin su girbi abin da suka shuka.

Katsinsa: Ɗan Shekara 22 Ya Sace Wa Dattijuwa Kuɗinta Na Garatuti Baki Daya, Ya Siya Mota Da Babur

A wani labarin, Yan sanda a Jihar Katsina, a ranar Litinin sun yi holen wani Aliyu Abdullahi mai shekaru 22, mazaunin Kasuwar Mata Street a Karamar Hukumar Funtua saboda damfarar wata tsohuwa.

Ya wawushe mata dukkan kudinta na garatuti ta hanyar amfani da katin ta na banki wato ATM inda ya siya mota da babur da kudin, Vanguard ta ruwaito.

An taba kama mayaudarin, wanda ya kware wurin damfarar mutane ta hanyar sauya musu katinsu na ATM a baya amma daga bisani ya fito daga gidan yari kuma ya cigaba da laifin, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Bindige Jigon Jam'iyyar PDP, An Garzaya Da Shi Asibiti

Asali: Legit.ng

Online view pixel