Kamfanonin sadarwa su na maganar kara farashin yin wayar salula saboda tsadar mai

Kamfanonin sadarwa su na maganar kara farashin yin wayar salula saboda tsadar mai

  • Idan dizil ya cigaba da wahala a gidajen mai, kamfanonin sadarwa su na iya kara kudin yin waya
  • Shugaban kungiyar Association of Licensed Telecoms Operators of Nigeria ne ya bayyana wannan
  • Mr. Gbenga Adebayo ya yi alkawarin za su dage sosai domin ganin ba a dakile hanyoyin sadarwa ba

Lagos - Kamfanonin da ke samar da hanyoyin sadarwa a kasar nan su na iya kara farashin yin waya muddin man dizil bai rage tsada a gidajen mai ba.

Punch ta tattauna da shugaban kungiyar Association of Licensed Telecoms Operators of Nigeria wanda ya nuna cewa babu mamaki a samu sauyin farashi.

Shugaban wannan kungiya, Gbenga Adebayo ya bayyana cewa dole kudin yin waya ya karu idan kamfanoni suka cigaba da sayen litar man dizil da tsada.

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Gbenga Adebayo ya ce kamfanonin sadarwa su na cikin wadanda suka fi kowa amfani da dizil a Najeriya don haka tsada da wahalar shi ya taba aikinsu.

Kawo yanzu, tsadar da man dizil ya yi da kuma wahalar samunsa a wurare da-dama na kasar nan ya taba kamfanonin sadarwar da suke aiki a Najeriya.

A wasu wuraren a yau, farashin kowane litan dizil ya haura N800, sannan man yana wahalar samu.

Kamfanonin sadarwa
Karafunan sadarwa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“Yanzu haka yana taba mu, kuma ya yi mana tasiri kwarai da gaske. Mu na cikin wadanda suka fi kowa aiki da man dizil a fadin kasar nan.”
“Ba a birane kurum mu ke amfani da shi ba; a ko ina a fadin kasar nan ne. Mu na bukatar dizil a duk inda ake amfani da hanyoyin sadarwa.”

Kara karanta wannan

Buhari Ya Nemi Afuwar Ƴan Najeriya Kan Ƙarancin Man Fetur Da Rashin Wutar Lantarki

“Kuma ba batun tsadan farashin ba ne kurum, har da wahalar samunsa. ‘Yan kasuwa sun fara shan wahalar kawo dizil saboda ya yi wuya.”

- Gbenga Adebayo

Za mu cigaba da aiki, amma ...

Rahoton ya ce Gbenga Adebayo ya shaidawa manema labarai cewa kamfanoni za su yi bakin kokarinsu wajen ganin ba a datse hanyoyin sadarwa ba.

Amma babu mamaki a ji farashi ya sauya idan aka cigaba da tafiya a irin wannan yanayin.

Abin babu tabbas a yau

“Lamarin dizil ya yi wahala a wannan lokaci. Mu na kokarinmu na ganin an cigaba da aiki. Abin da ba zan iya alkawari ba shi ne tashin kudin waya.”
“Ba zan iya bada tabbacin cewa nan gaba kadan ba za a samu canjn farashi ba. Ba zan iya bada tabbaci ba, ina jaddada cewa ba za mu yanke aiki ba.”

- Gbenga Adebayo

Kudin shan wuta ya karu

A makon nan ne aka ji cewa hukumar Nigerian Electricity Regulatory Commission ta ce farashin lantarki ya tashi daga watan Fubrairu bayan janye tallafin wuta.

Shugaban NERC na kasa, Sanusi Garba ya ce hakan ya biyo bayan janye tallafin lantarki da aka yi. An zo lokacin da gwamnatin tarayya ba za ta iya rangwame ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel