'Yan Bindiga Sun Bindige Jigon Jam'iyyar PDP A Wurin Taron Mutane

'Yan Bindiga Sun Bindige Jigon Jam'iyyar PDP A Wurin Taron Mutane

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai wa wani jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party hari a Jihar Edo

Isaiah Adanagbe, sakataren jam'iyyar a mazaba ta 9, karamar hukumar Oredo ya tafi wani shahararren mashaya ne da ya saba zuwa hira a yayin da abin ya faru

Bayan zamansa ya fara hira, kwatsam sai wasu da ake tunanin kwastoma ne suka taso suka lakada masa duka suka harbe shi da bindiga a kafa

Jihar Edo - Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun harbi wani jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a Jihar Edo, Isaiah Adanagbe, sakataren jam'iyyar a mazaba ta 9, karamar hukumar Oredo.

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Yan bindigan sun bindige Adanagbe ne a wani shahararren mashaya a kusa da Oza, Sokponba Road a Benin, The Punch ta ruwaito.

'Yan Bindiga Sun Bindige Jigon Jam'iyyar PDP, An Garzaya Da Shi Asibiti Rai A Hannun Allah
'Yan Bindiga Sun Bindige Jigon Jam'iyyar PDP, An Garzaya Da Shi Asibiti. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Wani wanda abin ya faru a idonsa a daren ranar Alhamis yace mutane sun kai masa dauki sun garzaya da shi asibiti nan take.

A halin yanzu ba a san dalilin da yasa aka kai masa harin ba duk da cewa Adanagbe dan siyasa ne da ake dama wa da shi kuma ya na yawan maganganu da dandalin sada zumunta.

"An bindige shi ne a daren ranar Alhamis kusa da Sakponba Road; shine sakataren mazaba ta 9 a Oredo.
"Ya zo wannan mashayar kamar yadda ya saba kuma an fara hira kowa na bayyana ra'ayinsa kwatsam sai wasu da muke tunanin kwastoma ne suka kai masa hari. Sun masa duka sannan suka harbe shi a kafa suka tafi.

Kara karanta wannan

Jerin yadda Sojoji 18, yan sanda 6 da yan Najeriya 76 suka rasa rayukansu cikin mako daya

"Mutane sun kawo masa dauki kuma an garzaya da shi asibiti domin yi masa magani. Yan uwansa sun tafi caji ofis na yan sanda domin kai rahoto," a cewar ganau din.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel