Putin ya tsure, ya tattara ma’aikata 1000 ya kora saboda tsoron a sa masa guba a Rasha

Putin ya tsure, ya tattara ma’aikata 1000 ya kora saboda tsoron a sa masa guba a Rasha

  • Ana zargin Vladimir Putin ya sallami da-dama daga cikin ma’aikatan da suke kusa da shi a Rasha
  • Mutane kusan 1,000 da su ke aiki a fadar Shugaban kasar na Rasha sun rasa hanyar cin abincinsu
  • Putin ya kori na-hannun damansa ne a dalilin tsoron magauta su sa masa guba domin su kashe shi

Russia - Shugaban Rasha yana cigaba da zama a cikin dar-dar na tsoron mutuwa. Rahotanni sun ce Vladimir Putin yana tsoron na-kusa da shi su kashe shi.

Wani rahoto da ya fito daga bakin Editan jaridar Daily Beast, Craig Copetas ya bayyana cewa Vladimir Putin yana sa mutane su dandana abinci kafin ya ci.

Editan ya bayyana cewa wannan tsoron mutuwa ne ya jawo shugaban na Rasha ya kori kusan mutane 1, 000 da ke aiki a karkashin domin bai yadda da su ba.

Kara karanta wannan

Kamfanonin sadarwa su na maganar kara farashin yin wayar salula saboda tsadar mai

Kamar yadda labari ya zo mana, Vladimir Putin ya yi maza ya nada wadanda za su maye gurbin ma’aikatan. Duk da haka yana yin taka-tsan-tsan da mutanensa.

Copetas ya ce tun daga masu sukola, zuwa sakatarori da masu dafa abinci, Putin ya yi waje da su, ya kawo sababbin mutanen da hankalinsa ya fi kwanciya da su.

Ba sabon abu ba ne wannan domin a kasar Rasha, an saba hallaka manyan mutane ta hanyar guba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Putin
Vladimir Putin da sojojin Rasha Hoto: www.japantimes.co.jp
Asali: UGC

Ba yau aka fara ba

Shugaba Vladimir Putin yana sane da cewa mutanensa ake zargi da laifin kashe ‘dan adawansa, Alexander Litvinenko ta hanyar sa masa guba a tukunyar shayi.

Haka zalika rahoton ya nuna cewa a shekarar 2018 wasu yaran Putin suka yi amfani da muguwar guba, suka kusa hallaka tsohon ‘dan leken asiri, Sergei Skripal.

Kara karanta wannan

Sheikh Zakzaky: Ina burin komawa Zariya na ci gaba da abin da nake yi a baya

Ba iyaka nan abin ya tsaya ba, shugaban na Rasha ake zargin ya tura dakaru su kashe Alexei Navalny da guba. Ba a dace ba amma duk da haka ya na kurkuku.

Tsoron sharrin magauta

Jaridar Marca ta ce Vladimir Putin ya fahimci matakan da ya dauka kwanan nan za su iya yin sanadiyyar da na hannun damansa za su nemi ganin bayansa.

Micheal Mc Faul ya na ganin hakan na nufin karshen mulkin Putin ya zo domin a haka ne daular kama-karya ta ke rushewa domin shugaba Putin ya fara tsurewa.

An kashe sojojin Rasha

Ku na da labari cewa Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce sun kashewa Rashawa sojoji kusan 1300 daga lokacin da aka soma yaki zuwa yanzu.

A cewar Mr. Volodymyr Zelensky kafin sojan Ukraine daya ya mutu, sai an kashewa Rasha sojoji goma. Zelensky ya ce duk da haka, ba abin da ya so kenan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel