Dubun wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi hanyar Kaduna-Abuja ya cika

Dubun wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi hanyar Kaduna-Abuja ya cika

  • Hukumar yan sandan ƙasar nan, ranar Alhamis, ta sanar da kame wani gawurtaccen ɗan bindiga da wasu mutum 26
  • A cewar yan sandan, mutumin mai suna Yellow Ashana, ya amsa cewa su ke addabar matafiya a hanyar Kaduna-Abuja
  • Wannan hanya dai ta yi ƙaurin suna wajen matsalar yan bindiga musamman garkuwa da mutane

Abuja - Rundunar yan sandan ƙasar nan ta bayyana cewa dakarunta sun yi ram da wani da ake zargin ƙasurgumin ɗan bindiga ne mai garkuwa da mutane, da wasu 26.

Rudunar yan sanda ta ce mutanen da suka shiga hannu suna daga cikin waɗan da suka fitini mutane da kai harin garkuwa da fashi da makami, musamman a babbar hanyar Kaduna-Abuja.

Nasarar yan sanda
Dubun wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi hanyar Kaduna-Abuja ya cika Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

A wata sanarwa da rundunar yan sandan Najeriya ta fitar ranar Alhamis da yamma a Twitter, kasurgumin ɗan bindigan dan kimanin shekara 36 ya amsa cewa shi ke jagorantar tawagarsu.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya lakaɗa wa Matarsa dukan kawo wuka har Lahira kan karamin abu

Wani sashin sanarwan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ɗaya daga cikin waɗan da aka kama shine Ahmed Yunusa wanda suke kira Yellowa Ashana, ɗan shekara 36. Shi ke jagorantar kungiyarsu suna aikata ta'addanci a hanyar Kaduna-Abuja."
"Wanda ake zargin ya amsa laifin cewa yana jagorantar tawagarsu wajen kai hari da garkuwa a hanyar, ya kuma ce sun kai hari sau uku kauyen Kadara a Kaduna, inda suka kashe mutane."

Yan ta'addan sun addabi hanyar Kaduna-Abuja

Wannan hanya ta Kaduna Zuwa Abuja ta yi kaurin suna wajen matsalar harin yan bindiga, da kuma garkuwa da matafiya, da fashi a wasu lokutan.

Yan ta'addan dake yawan kai hari kan babbar hanyar mai tara dandazon matafiya, kan mamaye su, sannan su tilasta musu tsayawa.

A lokuta da dama, yan ta'addan da babu tausayi a tattare da su, kan yi amfani da makamansu, su buɗe wa matafiya wuta domin tursasa su har su tsaya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun tattara maza da mata 47

Wasu mutane kan rasa rayukansu garin irin haka, wasu kuma Allah ya tseratar da su, yayin da kuma wasu sai yan uwansu sun biya fansa kafin yan ta'addan su sako su.

A wani labarin kuma Iyaye sun dawo daga kasar waje hutun shakatawa, sun taras ɗansu ya tafi yaƙi Ukraine

Wasu iyaye sun sha mamaki yayin da suka dawo gida daga hutun shaƙawa da suka tafi suka taras ɗan su baya nan.

Mahaifin matashin mai suna Adam, ya ce sun yi tsammanin zai zo ya ɗauke su a filin jirgi, amma sai faɗa musu ya yi ya tafi taimakawa Ukraine.

Asali: Legit.ng

Online view pixel