Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun aikata babbar ɓarna kan mutane

Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun aikata babbar ɓarna kan mutane

  • Yan ta'adda sun kai hari ƙauyen Agunu Dutse dake ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna da tsakar daren Alhamis
  • Bayanai daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun jikkata wani da harbi, sun kuma yi awon gaba da mutum 47
  • Har yanzun hukumomi a jihar Kaduna ba su fitar da wata sanarwa dangane da harin na baya-bayan nan ba

Kaduna - Yan ta'adda sun kai hari ƙauyen Agunu Dutse, dake ƙaramar hukumar Kachia jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da mutum 47 kuma suka jikkata wani ɗaya.

Wani mazaunin ƙauyen, Philp John, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch ya ce yan ta'addan sun shiga da daren ranar Ahamis misalin ƙarfe 1:00.

A cewarsa, ya bindigan sun zo da ɗumbin yawa kuma a ƙafa, suka rabu zuwa wurare Bakwai kuma suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mutane.

Kara karanta wannan

Yan sanda da Sojoji sun yi wa yan bindiga rubdugu a Abuja, sun ceto mutum ɗaya

Yan bindiga a Kaduna
Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun aikata babbar ɓarna kan mutane Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya kuma yi bayanin cewa ƙauyen da lamarin ya faru na da nisan kilomita biyu kacal tsakaninsa da Barikin sojojin Akada.

Daily Trust ta rahoto John ya ce:

"Waɗan da suka sace sun haɗa da maza 16, ƙananan yara Tara da kuma mata 32. Mutanen garin ba zasu iya hana maharan ba saboda muggan makaman dake tattare da su."
"Har yanzun masu garkuwan da suka aikata haka ba su tuntubi kowa ba bare jin halin da mutanen ke ciki."

Shin jami'an tsaro suna da rahoton abin da ya faru?

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, Mohammed Jalige, bai ɗaga kiran wayar da aka masa ba, kazalika bai turo amsoshin sakon da aka tura masa ba.

Haka nan, har yanzu da muka tattara wannan rahoton, hukumomi a jihar Kaduna ba su ce uffan ba game da sabon harin da yan ta'dda suka kai.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun mamayi Jami'an gidan Yari, sun halaka fiye da ɗaya

A wani labarin kuma Jirgin yakin NAF ya yi luguden wuta a wurin shagalin auren kasurgumin ɗan bindiga, rayuka sun salwanta

Jirgin yaƙin rundunar sojin sama ya yi luguden wuta kan wurin shagalin bikin wani kasurgumin ɗan bindiga a Katsina.

Bayanai sun bayyana cewa luguden wutan ya yi wa yan ta'adda mummunan ɓarna, ya tura manyan su barzahu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel