Wani bawan Allah ya lakaɗa wa Matarsa dukan kawo wuka har Lahira kan karamin abu

Wani bawan Allah ya lakaɗa wa Matarsa dukan kawo wuka har Lahira kan karamin abu

  • Wani Magidanci ya halaka matarsa ta hanyar lakaɗa mata dukan kawo wuka kan wani karamin saɓani da ya haɗa su
  • Lamarin wanda ya faru a jihar Delta, ya sa Mutumin tsere wa, amma dakarun yan sanda suka nemo shi kuma suka damƙe shi
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar Delta ya ce hukumarsu na gudanar da bincike dan gano ainihin abinda ya faru

Delta - Wani magidanci ɗan shekara 42, Efe Erinoja, ya shiga komar yan sanda bisa zargin lakaɗa wa matarsa dukan tsiya har Allah ya karɓi rayuwarta a Orerokpe, karamar hukumar Okpe, jihar Delta.

Jaridar Punch ta tattaro cewa wanda ake zargin ya aikata wannan ɗanyen aiki ne ranar Laraba da misalin ƙarfe 6:30 na safe bayan wani karamin saɓani ya shiga tsakanin su.

Duk da babu bayani kan ainihin abin da ya haɗa su, Majiya daga yankin ta bayyana cewa kukan matar mai suna Faith Ekpe, yar shekara 36 ne ya sa mutanen makota suka farga.

Kara karanta wannan

Kungiya a arewa ta lale miliyoyi ta siyawa Atiku Abubakar Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a 2023

Taswirar jihar Delta
Wani bawan Allah ya lakaɗa wa Matarsa dukan kawo wuka har Lahira kan karamin abu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sai dai bisa rashin sa'a, Lokacin da mutane suka isa gidan mutumin tuni Faith ta riga ta ce ga garin ku nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da Mijin ya tabbatar da ɗanyen aikin da ya aikata, bai yi wata-wata ba ya tsere daga yankin, aka daina ganinsa baki ɗaya.

Wane mataki mutane suka ɗauka?

Ɗan uwan mamaciyar mai suna, Monday Ekpe, ya gaggauta kai rahoton abin da ya faru caji ofis ɗin yan sanda dake Orerokpe.

Yan sanda sun isa wurin da abun ya faru kuma suka tarad da gawar matar kwance da tabon jibgar da ta sha a sassan jikinta.

Jami'an yan sandan sun ɗauke gawar daga wurin, suka kaita ɗakin aje gawarwaki na Ariemughere, Orerokpe domin gwajin da ya dace.

Wata majiya a hukumar yan sanda ta tabbatar da cewa daga baya sun bibiya inda mutumin ya ɓuya, kuma suka yi ram da shi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun tattara maza da mata 47

Wane hali ake ciki yanzu?

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Delta, DDP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce suna cigaba da bincike.

Ya ce:

"Tuni yan sanda suka fara gudanar da bincike kan musabbabin da ya haɗa ma'auratar rikici har haka ta faru."

A wani labarin na kuma Uwar gida ta danna wa Mijinta wuka har lahira daga zuwa bankwana zai koma dakin Amarya

Tsagwaron kishin mata ya yi sanadin rasuwar wani Mai mata biyu yayin da yake yi wa Uwar gida bankwana zai koma dakin Amarya.

Rahoto ya nuna cewa Uwar gidan mai suna Atika ta daba wa mijinsu wuka har lahira a Mararaba dake jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel