Tashin Hankali: Iyaye sun dawo daga kasar waje hutun shakatawa, sun taras ɗansu ya tafi yaƙi Ukraine

Tashin Hankali: Iyaye sun dawo daga kasar waje hutun shakatawa, sun taras ɗansu ya tafi yaƙi Ukraine

  • Wasu iyaye sun sha mamaki yayin da suka dawo gida daga hutun shaƙatawa da suka tafi suka taras ɗan su baya nan
  • Mahaifin matashin mai suna Adam, ya ce sun yi tsammanin zai zo ya ɗauke su a filin jirgi, amma sai faɗa musu ya yi ya tafi taimakawa Ukraine
  • A cewar Mahaifinsa, Mista Ennis, sun shiga damuwa matuƙa amma ɗansu ya yanke hukuncin da ya dace

Iyayen wani mai gareji a ƙasar Scotland sun bayyana cewa sun gano ɗansu ya tafi taimakawa Ukraine bayan rashin ganinsa ya zo ɗaukarsu a Filin jirgi yayin da suka dawo daga hutu.

Vanguard ta rahoto cewa Adam Ennis, ɗan shekara 35 daga Biggar, kudu maso yammacin Edinburgh ya bar Scotland domin haɗuwa da tawagar mutum 50 daga sassan duniya da zasu taimaka wajen kare birnin Kyiv.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya lakaɗa wa Matarsa dukan kawo wuka har Lahira kan karamin abu

Rasha da Ukraine
Tashin Hankali: Iyaye sun dawo daga kasar waje hutun shakatawa, sun taras ɗansu ya tafi yaƙi Ukraine Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Mahaifinsa Brian Ennis, ya tafi Thailand tare da matarsa da kuma ɗiyarsa domin hutun shakatawa inda suka shafe watanni uku a can.

Mahaifin matashin ya shaida wa BBC ta kasar Scotland cewa sun kaɗu matuƙa da suka tabbatar da ɗan su ya tafi filin yaƙi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Nation ta rahoto A jawabinsa, Ennis ya ce:

"Mun zaci Adam ne zai zo ya ɗauke mu a Filin jirgi amma bisa mamaki sai abokinsa ne ya zo ɗaukar mu a maimakonsa. Abokinsa bai faɗa mana komai ba, har sai lokacin da Adam ya kira mu ta wayar salula."
"Ba mu san ya tafi ba har sai da yammacin nan da ya kira mu. Yanzu haka yana can ƙasar Ukraine a wani sansani."

Shin dama Adam na da kwarewar yaƙi?

Matashin ba shi da kwarewar aikin Sojoji amma mahaifinsa ya ce yasan ɗansa ya iya rike bindiga da kuma sarrafata.

Kara karanta wannan

'Zan cika burin yan Najeriya' Matashi dan shekara 45 ya shiga tseren gaje kujerar Buhari a 2023

Mista Ennis ya ce ya damu sosai da lafiyar ɗansa amma kuma ya na alfahari da matakin da ya ɗauka na zuwa ya taimaka wa Ukraine.

"Kamar kowane Uba, ba zaka so ganin wanda kake so ya shiga hatsari ba kuma tunaninsa ya hana mu bacci lokuta da dama."
"Mun damu sosai amma ya yi abu mai kyau. Ba wai ya tafi can dan ya samu ɗaukaka bane, kuma nasan bai yi dana sanin zuwa ba."

A wani labarin kuma Ko kunsan kasashen da Musulmai zasu yi dogon Azumi da kasashen da zasu yi gajere a bana Ramadan 2022?

Biliyoyin al'ummar Musulmai a faɗin duniya na gab da shiga wata mai Albarka Ramadan na shekarar 2022.

Musulman wasu ƙasashe za su fuskanci dogon Azumi na tsawon awanni a bana, yayin da wasu kuma za su yi gajere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel