Kudi sun samu: Najeriya ta sayar da danyen mai na N14.4trn a 2021 ga wasu kasashe 5

Kudi sun samu: Najeriya ta sayar da danyen mai na N14.4trn a 2021 ga wasu kasashe 5

 • Kudaden shiga na danyen man fetur da gwamnatin tarayya ta samu ya inganta a 2021 inda ya kai Naira tiriliyan 14 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 9.44 da aka sayar 2020
 • Danyen mai shi ne babban abin da Najeriya ke fitarwa zuwa kasashen waje kuma yana wakiltar babbar hanyar da gwamnatin tarayyar Najeriya ke samun daloli
 • Indiya ta kasance babbar abokiyar cinikayyar Najeriya ta fuskar danyen mai kuma ta kashe sama da tiriliyan daya don siyan man Najeriya a matatunta

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa Najeriya a 2021 ta samu sama da Naira tiriliyan 14.4 na kudin danyen mai daga kasashe daban-daban na duniya.

NBS ta bayyana hakan ne a cikin sabon rahotonta na kididdigar cinikayyar kasashen waje da aka buga a shafinta na yanar gizo a ranar Talata, 15 ga Maris, 2021.

Kara karanta wannan

Tattalin arziki: Najeriya na fuskantar barazanar asarar sama da Naira Biliyan 1 a kullum

Danyen mai a Najeriya
Kudi sun samu: Najeriya ta sayar da danyen mai na N14.4trn a 2021 ga wasu kasashe 5 | Hoto: nairametrics.com

Bisa kididdigar da aka yi, an ce cinikin danyen mai ya kai aU 76.22 na jimillar fitar da man da aka yi a cikin shekarar da aka yi nazari a kai.

Manyan kasashe 5 da suka fi sayen man Najeriya

Rahoton ya nuna cewa Indiya ce ta jagoranci jadawalin kasashe biyar da suka sayi danyen man Najeriya bayan da ta sayi mai na sama da Naira tiriliyan 1.98.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kasar da ta biyo baya ta kashe Naira tiriliyan 1.44; wato Spain a shekara kan danyen man na Najeriya yayin da kuma ta zo a matsayi na uku da sayan na Naira biliyan 863.3.

Kasashe biyar da za su cika jerin sune Kanada da Amurka yayin da suka kashe Naira biliyan 422.7 da kuma Naira biliyan 400 wajen siyan danyen mai na Najeriya.

Manyan kasashe 10 da aka yi harkalla dasu a cikin watanni uku na karshe na 2021

Kara karanta wannan

Ukraine: Hotunan 'Yan Najeriya 121 Da Suka Iso Daga Poland Cikinsu Har Da Jinjiri

Rahoton na NBS ya kuma lissafa adadin kudaden da kasashe suka kashe a cikin watanni uku na karshen 2021 (Oktoba zuwa Disamba) domin sayen danyen man fetur na Najeriya.

Ga kasashen kamar haka:

 1. Indiya - N774.5bn
 2. Spain - N624.01bn
 3. Faransa- N473.84bn
 4. Netherlands- N383.58bn
 5. Indonesia- Naira biliyan 280.05
 6. Afirka ta Kudu- N251bn
 7. China- Naira biliyan 92.73
 8. Amurka- Naira biliyan 171.08
 9. Kanada- Naira biliyan 216.13

Tsabar kudi: Dangote ya tsallake matsayi mai girma, ya dara attajirai 429 da ake ji dasu a duniya

A wani labarin, attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, kuma shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote na Najeriya, ya zuwa ranar Laraba, 9 ga Maris, 2022 ya zama mutum na 71 mafi arziki a duniya sabanin matsayinsa na 100 da a farkon 2022.

A yanzu dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 20.1, bayan da ya tara dala miliyan 914 (N380bn) cikin kankanin lokaci, a cewar rahoton kididdigar hamshakan masu kudi na Bloomberg.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur: Najeriya na da mai sama da lita 1.9bn a boye, ministan Buhari

Hamshakin attajirin nan dan kasar Afrika ta kudu Johann Rupert yana matsayi na 221 a jerin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya, inda arzikinsa ya kai dala biliyan 9. Hakan ya nuna cewa, Dangote ya ninka shi sau biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel