Tsabar kudi: Dangote ya tsallake matsayi mai girma, ya dara attajirai 429 da ake ji dasu a duniya

Tsabar kudi: Dangote ya tsallake matsayi mai girma, ya dara attajirai 429 da ake ji dasu a duniya

  • Matsayin Dangote a cikin manyan attajiran duniya na karuwa yayin da mafi yawan hamshakan attajiran da ke kusa da shi ke asarar dukiyoyinsu sakamakon yakin Rasha da Ukraine
  • Tun daga farkon 2022, Dangote ya tsallake matsayi na 29 a kididdigar masu kudin duniya na rahoton Bloomberg
  • Dangote wanda a halin yanzu ya mallaki $20.1bn, wanda a yanzu ya ninka dala biliyan 9.47 na hamshakin attajirin Afirka ta Kudu, Kudu kuma na biyu mafi arziki a Afirka

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, kuma shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote na Najeriya, ya zuwa ranar Laraba, 9 ga Maris, 2022 ya zama mutum na 71 mafi arziki a duniya sabanin matsayinsa na 100 da a farkon 2022.

A yanzu dukiyarsa ta kai dalar Amurka biliyan 20.1, bayan da ya tara dala miliyan 914 (N380bn) cikin kankanin lokaci, a cewar rahoton kididdigar hamshakan masu kudi na Bloomberg.

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Yadda Dangote ke kara shillawa sama
Tsabar kudi: Dangote ya tsallake matsayi mai girma, ya dara attajirai 429 da ake ji dasu a duniya | Hoto: Bloomberg
Asali: Facebook

Hamshakin attajirin nan dan kasar Afrika ta kudu Johann Rupert yana matsayi na 221 a jerin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya, inda arzikinsa ya kai dala biliyan 9. Hakan ya nuna cewa, Dangote ya ninka shi sau biyu.

Rupert ya yi asarar sama da dala biliyan 1 tun bayan da yakin Ukraine da Rasha ya barke. Sakamakon kalubalen da fuskanta a harkallar kasuwancin kayansa na alatu.

A wani lokaci a 2022, arzikin Rupert ya kara habaka da sauri yayin da arzikin Dangote ke raguwa, lamarin da ya sa manazarta da dama ke ganin cewa za a iya samun canjin a duniyarsa a karshen 2022.

Arziki nufin Allah: Yadda karin arzikin Dangote ke ba da citta

Ana sa ran arzikin Dangote zai bunkasa a watanni masu zuwa yayin da yake gab kammala aikinsa na matatar mai dake Legas.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan yan sanda sun kama yan bindiga 200, yan fashi 20 a jihar Kaduna

Matatar man za ta zama kari kan jerin hannayen jarin Dangote, da suka hada da siminti, Sukari, jarinsa a kamfanin Nascon Allied, da wani hannun jari a bankin United Bank for Africa.

Kazalika, masana’antun Dangote sun mallaki sana’o’in da ke da hannu mai kwabi a harkallar samar da abinci, da taki, da mai da sauran abubuwan rayuwa na yau da kullum.

Sunayen wasu 'yan Afirka dake cikin jerin masu kudin duniya 500 na Bloomberg

241- Nicky Oppenheimer ($8.78bn)

451- Nassef Sawiris ($5.57bn)

490- Naguib Sawiris ($5.22bn)

Ba iya nan ba

A halin da ake ciki kuma, a cewar Bloomberg, Dangote a yanzu ya fi mai Chelsea Roman Abramovich arziki kusan sau biyu, wanda ke kan matsayi na 129 da tarin dukiyar da ta kai dala biliyan 13.6.

Yakin Ukraine da Rasha: Burtaniya ta daskarar da kadarorin mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea

A wani labarin na daban, kasar Burtaniya ta daskarar da kadarorin mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich, kana ta sanya haramcin mu'amala da daidaikun mutane da 'yan kasuwa na Burtaniya, da dokar hana zirga-zirga duk dai akansa.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa a yaki

Sky Sports ta rahoto Firayim Ministan Burtaniya, Boris Johnson yana cewa:

"Ba zai yiwu a samar da mafaka ga wadanda suka goyi bayan mummunan harin da Putin ya kai wa Ukraine ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel