Ukraine: Hotunan 'Yan Najeriya 121 Da Suka Iso Daga Poland Cikinsu Har Da Jinjiri

Ukraine: Hotunan 'Yan Najeriya 121 Da Suka Iso Daga Poland Cikinsu Har Da Jinjiri

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake kwaso wasu yan Najeriya guda 122 daga kasar Poland cikinsu har jinjiri guda daya
  • Bayan isarsu filin tashi da saukan jirage na Nnamdi Azikwe da ke Legas a jirgin Airpeace, an basu kyautan layin waya da katin N5000 da dalar Amurka 100
  • Tun bayan da Rasha ta afka wa Ukraine da yaki, fararen hula yan Najeriya da wasu kasashen sun rika ficewa daga kasar domin komawa kasashensu na asali

Sakamakon yakin da Rasha ta afkawa Ukraine da shi, an sake kwaso wasu tawagar yan Najeriya daga kasar Poland, inda suka tafi suka fake, kafin a dawo da su kasarsu.

Yan Najeriya su 122, har da jinjiri sun iso filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja misalin karfe 1.12 na daren Alhamis.

Kara karanta wannan

An tasa keyar dan adawan Ganduje, Dan Bilki Kwamanda, gidan gyara hali

Ukraine: Hotunan 'Yan Najeriya 121 da Suka Iso Daga Poland Cikinsu Har da Jinjiri
Ukraine: Hotunan 'Yan Najeriya 121 Da Suka Iso Daga Poland Cikinsu Har da Jinjiri. Hoto: @nidcom_gov
Asali: Twitter

An sanar da hakan ne ta shafin Twitter na Hukumar Kula da Yan Najeriya mazauna kasashen waje.

NiDCOM ta rubuta:

"Kaso na biyu na yan Najeriya da aka kwaso daga Warsaw, Poland su 122, da jinjiri sun iso filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe a yau Juma'a 11 ga watan Maris, 2022 a jirgin Air Peace misalin 1.20 na safe.
"Kawo yanzu an kwaso mutane 1,199 daga Ukraine.
"An bawa wadanda suka dawo kyautar layin waya da kudi N5000 domin su samu damar kiran yan uwansu a wani hadin gwiwa tsakanin NiDCOM da MTN da dalar Amurka 100 a matsayin kudin mota daga gwamnatin tarayyar Najeriya."

Ga hotunan wadanda suka dawo din a kasa:

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel