Tsadar man fetur: Najeriya na da mai sama da lita 1.9bn a boye, ministan Buhari

Tsadar man fetur: Najeriya na da mai sama da lita 1.9bn a boye, ministan Buhari

  • Yanzu haka Najeriya tana da lita biliyan 1.9 na man fetur a cewar karamin ministan albarkatun man fetur na Najeriya, Mista Timipre Sylva
  • Ministan ya yi ikirarin cewa lita biliyan 1.9 na man fetur na iya gamsar da kasar na tsawon kwanaki 32
  • Sylva ya bayyana haka ne a Abuja yayin da yake magana a gaban majalisar zartarwa ta tarayya a zaman da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta

Timipre Sylva, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur ya bayyana cewa yanzu haka Najeriya na da lita biliyan 1.9 na man fetur a ajiye.

A cewarsa, wannan mai na iya gamsar da bukatun kasar na tsawon kwanaki 32, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Karamin minista ya bayyana yawan man fetur a Najeriya
Tsadar man fetur: Najeriya na da mai sama da lita 1.9bn a boye, ministan Buhari | Hoto: tvcnews.tv
Asali: Twitter

Ministan ya bayyana haka ne jiya Laraba 9 ga watan Maris a Abuja yayin da yake magana a gaban majalisar zartarwa ta tarayya a zaman da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Sai irin su Buhari: Osinbajo ya bayyana wanda iya zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Babban Manajin Darakta na Kamfanin Mai na Najeriya Mista Mele Kyari ya raka shi a taron na FEC da aka yi.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa, ofishin mataimakin shugaban kasa, Mista Laolu Akande ne ya bayyana haka bayan taron.

Vanguard ta Akande yana cewa:

“Akwai lodin sa’o’i 24 da ke gudana a dukkan gidajen man da ke aiki tare da Hukumar Ma’aikatar Jiha da kuma Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya don tabbatar da cewa lamarin ya daidaita yadda ya kamata.”

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

A wani labarin, ‘yan Najeriya sun tafi shafukan sada zumunta domin nuna damuwa, bacin rai da kuma fusata kan karancin man fetur da ke kara ci gaba da dabaibaye wasu sassan kasar nan.

Kara karanta wannan

Buhari ya bayyana mutum 3 da za su cigaba da rike madafan iko har ya dawo daga Ingila

An ga dogayen layukan da aka yi a safiyar yau a wasu sassan Legas da Abuja, lamarin da ya sa masu ababen hawa kokawa da hawan farashin mai a daidai lokacin da matsalar karancin abinci ke kara kamari.

Wani mashahurin Fasto @Olubankoleidowu, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Mun shiga uku! Wannan sabon karancin man fetur yana tunatar da mu wace shawara ya kamata mu yanke a 2023. ’yan Najeriya ku bi a hankali. Allah ba zai sauko daga sama domin ya muku yaki ba, shi ya sa ya ba ku kwakwalwa.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel