Katoɓarar Da Wike Ya Yi Game Da Ɗan Fodio Ya Janyo Masa Fushin 'Yan Arewa

Katoɓarar Da Wike Ya Yi Game Da Ɗan Fodio Ya Janyo Masa Fushin 'Yan Arewa

  • Wata kungiyar Arewa ta ragargaji Gwamna Wike kan katoɓara da maganganu ya rashin ɗa'a da ya yi game Sheikh Usman Ɗan Fodio da kuma wasu yan jam'iyyar PDP
  • Ƙungiyar ta nuna takaicinta kan yadda Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto da takwararsa Bala Mohammed na Bauchi suka yi shiru yayin da Wike ke yawaita maganganu na cin mutunci
  • Ƙungiyar ta bukaci Gwamna Wike ya janye kalamansa na rashin ɗa'ar sannan ya bada hakuri idan ba haka ba za ta hukunta shi

Abuja - Wata kungiyar Arewa na hadin kan ƙasa, 'Northern Alliance for National Cohesion, NANC, a ranar Talata ta bukaci gwamnan Rivers Nyesome Wike ya janye kalaman da ya yi na danganta wani mai sarautar gargajiya a jiharsa Sheikh Uthman Dan Fodio, kuma ya bada hakuri nan take.

Kara karanta wannan

2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

Hakan na zuwa ne yayin da kungiyar ta ke kawar da game da maganganu marasa dadi da Wike ya fadi kangwamnan Edo Godwin Obaseki da mataimakinsa, Hon. Philip Shaibu, rahoton Vanguard.

Katoɓarar Da Wike Ya Yi Game Da Ɗan Fodio Ya Janyo Masa Fushin 'Yan Arewa
Maganganu Da Wike Ya Yi Game Da Ɗan Fodio Ya Janyo Masa Fushin 'Yan Arewa. Hoto: Vanguard Nigeria
Asali: Twitter

Kungiyar arewan ta yi kira ga gwamnoni su ja kunnen Wike

Kungiyar ta yi kira ga gwamnonin Arewa da shugabannin PDP su ja kunnen Wike, ta kuma yi barazanar daukan mataki kan gwamnan idan bai bada hakuri ba bisa kalamansa.

Da ya ke magana da manema labarai a Abuja, shugaban kungiyar, Bello Ibrahim, ya ce,

"An janyo hankalin mu kan wasu maganganu na rashin mutunci da mai girma Gwamnan Rivers Nyesome Wike ya yi, inda a fili ya soki wasu shugabannin mu, yan jam'iyya da wasu masu ruwa da tsaki a PDP.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

"A jiya ma, Gwamna Wike kamar yadda ya saba, ya soki Mataimakin Gwamnan Edo, Hon Philip Shaibu, saboda bayyana ra'ayinsa a gaban kwamitin ayyuka na jam'iyya na ƙasa da suka tafi jiharsa yin wasu ayyuka.
"Duk da hakan, Wike ya kuma soki Gwamnan Edo, Mr Godwin Obaseki saboda mayar masa martani game da wasu abubuwa da suka shafi hadin kan jam'iyya.
"Abin takaici ne idan aka tuna lokacin da Wike ya ci mutuncin Sheikh Usman Dan Fodio a wani wurin taro. An ga Wike yana kwatanta daya daga cikin sarakunan jiharsa da mutum mai daraja irin Sheikh Dan Fodio. Wannan shine kalamai mafi muni da aka furta game da Dan Fodio daga kudancin Najeriya a baya-bayan nan.
"Wike ya nuna rashin girmamawa ga dokar jam'iyya, inda a baya-bayan nan ya yi barazanar daukan wasu matakai a kudin tsarin mulkin jam'iyyar idan shugaban jam'iyyar na ƙasa bai hukunta mataimakin gwamnan jihar Edo - Philip Shaibu ba. Abin dariya ne duba da cewa Gwamna Wike shine ja gaba wurin nasarar Ali Modu Sheriff wanda ya kusa durkusar da jam'iyyar amma shi ne yanzu ke son yin wa'azi."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tsagin Mala Buni ya kwace ikonsa a Hedkwatar APC, ya faɗi gaskiyar abun da ya faru

Sanarwar ta cigaba da cewa ya kamata a lura cewa Wike ya saba cin mutuncin takwarorinsa gwamnoni, yana daukan kansa gaba da kowa amma abubuwan da ya ke aikatawa sun saɓa tsari.

Shirun da Tabuwal da Bala Mohammed suka yi game da cin mutuncn Dan Fodio ya bamu mamaki, Kungiyar Arewa

Hakazalika, Kungiyar ta ce abin damuwa ne ganin yadda Gwamnoni kamar Aminu Waziri Tambuwal da Bala Mohammed Abdulkadir na Jihar Bauchi suka yi tsit yayin da Wike ya kwatanta mai sarautar gargajiya a Rivers da Sheikh Dan Fodio. Yin shiru na nuna ragwancinsu ne ko kuma suna goyon bayan abin da ya ke yi.

Ya yi watsi da karamci da mutunci wurin yin mu'amula da mutane a cewar jam'iyyar, a lokacin da ake bukatar haɗin kai da zaman lafiya a kasa.

Don haka kungiyar ta bukaci Wike ya janye maganarsa nan take game da Dan Fodio, ya kuma bada hakuri, sannan gwamnonin arewa da manyan yan siyasa su nesanta kansu da kalamansa marasa dadi idan har ba suna son ya ruguza jam'iyyar bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel