Da Dumi-Dumi: Mutanen Mala Buni sun dawo ikonsu a Hedkwatar APC, sun jinjina wa INEC

Da Dumi-Dumi: Mutanen Mala Buni sun dawo ikonsu a Hedkwatar APC, sun jinjina wa INEC

  • Kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin Gwamna Buni na Yobe ya sake dawo da ƙarfinsa a hedkwatar APC ta ƙasa
  • Sakataren kwamitin na kasa, Sanata Akpanudoedehe, ya koma bakin aiki bayan jita-jitar ya yi murabus ko an canza shi
  • Kazalika APC ta fitar da sanarwa mai kunshe da bayani kan abin da ya faru makon da ya gabata, tace babu wani rikici

Abuja - Alamomi na nuni da cewa yunkurin da wasu suka yi na tsige Mai Mala Buni daga shugabancin kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa ya faɗi warwas.

Sakataren kwamitin, Sanata John James Akpanudoedehe, wanda ke jagorantar kwamitin idan Buni baya nan, ya koma bakin aiki, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Abubakar Bello na Neja ne ya karɓi ragamar tafiyar da jam'iyya, yayin da Malam El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana cewa Mala Buni ba zai sake dawo wa kujerar shugaba ba.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kalubalen da bangaren su Shekarau za su fuskanta a siyasa kafin zaben 2023

Gwamna Mala Buni
Da Dumi-Dumi: Mutanen Mala Buni sun dawo ikonsu a Hedkwatar APC, sun jinjina wa INEC Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta ƙi amincewa da jagorancin Bello, wanda hakan ya tilasta wa masu ruwa da tsaki na APC canza tunani.

Amma da yammacin yau Talata, Sakataren kwamitin rikon kwarya na ƙasa, Sanata Akpanudoedehe, ya koma bakin aiki a Sakatariyar dake Abuja.

A wata sanarwa da ya fitar bayan komawa bakin aiki ranar Talata, Sakataren APC yace jam'iyyarsu a dunƙule take kuma tana nan da ƙarfinta.

The Cable ta rahoto Sakataren ya ce:

"Kwamitin rikon kwarya (CECPC) ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamna Mala Buni na Yobe, ya fitar da jawabi domin kore tantamar abin da ya faru makon da ya gabata.
"Kuma muna tabbatarwa mambobi da masu ruwa da tsaki na jam'iyya, da sauran yan Najeriya cewa babu wani rikici a APC, muna nan da karfi kuma a dunkule domin sauke nauyin da muka ɗauka."

Kara karanta wannan

Rikici APC: Gwamna ya yi amai ya lashe, ya ce har yanzun Buni ne shugaban APC ta kasa

"Tun ranar 28 ga watan Fabrairu, shugaban kwamiti ya tafi doguwar tafiya ta duba lafiya, ya bar rubutaccen umarni mambobi su cigaba da harkokin jam'iyya duk da baya nan, musamman ayyukan yau da kullum."

Bugu da ƙari, ya bayyana cewa an cigaba da gudanar da ayyukan jam'iyya don kokarin bin jadawalin zaɓen 2023 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta fitar.

Shin ina maganar tsige Buni ta kwana?

Akpanudoedehehttps ya ce duk abin da ya faru ya saba faruwa da nufin riko idan Mala Buni baya nan, ba kamar yadda mutane sukai ta yaɗa wa cewa an tsige Buni da wasu kusoshin CECPC.

"Mun jinjina wa INEC bisa kokarinta na ganin ba mu kauce hanya ba ta kowane yanayi. A halin yanzu, APC ta haɗa manyan lauyoyi domin shawo kan hukuncin Kotu na dakatar da babban taronta na ƙasa."

A wani labarin kuma Gwamoni jam'iyyar PDP biyu sun barke da rikici mai zafi, sun fara kiran juna 'Ma ci Amana'

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Ɗiyar Bola Tinubu ta yi tsokaci kan shirin mahaifinta na gaje kujerar Buhari

Rikici tsakanin gwamnonin jam'iyyar PDP biyu ya kara tsananta, Wike ya kara mauda wa Obaseki martani mai zafi.

Wike ya roki tsohon shugaban APC na ƙasa gafara bisa kin ɗaukar gargaɗinsa game da halayen gwamna Obaseki na Edo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel