2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

Yayin da gangar siyasa ya fara kadawa a kasar, yan siyasa a fadin kasar sun fara zage damtse tare da neman tudun dafawa domin ganin sun cimma kudirorinsu gabannin babban zaben 2023.

A jihar Kaduna, zuwa yanzu an samu wasu manyan yan siyasa da suka fito suka ayyana aniyarsu ta neman kujerar Gwamna Nasir El-Rufai na jihar.

2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu
2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu Hoto: The Punch/Daily trust/Twitter/@kudan_isa/Facebook /Shehu Sani
Asali: UGC

Legit Hausa ta tattaro maku jerin yan siyasa biyar da suka riga suka ayyana aniyarsu na neman kujerar gwamnan na jihar Kaduna.

1. Shehu Sani

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, yace zai nemi kujerar gwamnan jihar Kaduna karkashin inuwan jam'iyyar PDP a babban zaɓen 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

Shehu Sani ya shaida wa manema labarai cewa ba bisa ra'ayin kansa ne zai tsaya takarar gwamnan ba, mutane ne suka nemi ya yi hakan, BBC Hausa ta rahoto.

2. Isa Ashiru

Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2019, Hon Isa Kudan Ashiru ya ce shi ya samu nasara a zaben 2019 amma magudi aka tafka masa, amma zai kara tsayawa takarar a shekarar 2023, Vanguard ta ruwaito.

Ya kara da cewa yana siyasa ne don yi wa mutane aiki sannan ya shayar da jama’ansa romon dimokradiyya.

3. Muhammed Sani Datijjo

Muhammed Sani Datijjo, Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na Jihar Kaduna shima ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan jihar a babban zaben 2023.

Dattijo ya shaida hakan a wata wallafa da ya yi a Facebook ranar Talata, 15 ga watan Maris.

4. Uba Sani

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Uba Sani ya bayyana kudurinsa na neman kujerar gwamnan Kaduna a APC a 2023

Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Uba Sani, ya bayyana aniyarsa ta neman takarar gwamnan Kaduna a 2023.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Uba ya bayyana haka ne a Sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Kaduna a ranar Talata, 15 ga watan Maris.

5. Abdulmalik Mohammed Durungwa

Dr Abdulmalik Mohammed Durungwa, shima ya nuna sha’awarsa ga kujerar inda ya roki Gwamna Nasir Ahmed El-rufai da ya mara masa baya gabannin zaben.

Durungwa ya roki El-Rufai da ya goyi bayan mika kujerar gwamnan jihar na APC zuwa yankin kudancin Kaduna.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ya yi rokon ne a ranar Litinin a wani taro da kungiyar yan jarida na kudancin Kaduna, inda ya ayyana aniyarsa ta takarar kujerar a hukumance.

Gwamnan APC ya canza magana, ya ce har yanzun Mala Buni ne shugaban APC na ƙasa

A wani labari na daban, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, yace har yanzu takwaransa na jihar Yobe, Mala Buni, ne shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kalubalen da bangaren su Shekarau za su fuskanta a siyasa kafin zaben 2023

Kujerar Buni ta shiga rububi a makon da ya gabata, bayan gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya karbi jagorancin jam'iyya.

Gwamna Bello ya maye gurbin shugaban jam'iyya ne bayan gwamna Buni ya tafi Dubai a duba lafiyarsa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel