2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

2023: Bayan Uba Sani, Kwamishina a Kaduna Ya Ce Shima Yana Son Ya Gaji El-Rufai

  • Kwamishinan tsare-tsare da kasafin Kudi na Jihar Kaduna, Muhammad Dattijo, ya bayyana kudirinsa na gadar kujerar gwamna Nasir El-Rufai a 2023
  • Dattijon da ba a dade da ba shi mukami ba a jami’ar kasuwanci ta Henly da ke Ingila ba, ya shaida hakan a ranar Talata a wata wallafar da ya yi a Facebook
  • A cewarsa yanzu zai fara kamfen din neman kujerar gwamna kuma yana da yakinin cin nasara musamman idan mutane suka duba ayyukan da ya yi wa jihar

Jihar Kaduna - Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na Jihar Kaduna, Muhammad Dattijo, ya bayyana kudirin sa na maye gurbin Gwamna Nasir El-Rufai a 2023, The Punch ta ruwaito.

Dattijo, wanda makarantar kasuwanci ta Henley da ke Jami’ar Reading a Ingila ba ta dade da ba shi mukami ba a cibiyar Dunning Africa, ya shaida hakan a wata wallafa da ya yi a Facebook ranar Talata.

Kara karanta wannan

2023: Jerin mutane 5 da suka bayyana aniyarsu ta yin takarar gujerar gwamnan Kaduna zuwa yanzu

2023: Ina Son in Gaji El-Rufai, Kwamishinan Jihar Kaduna
2023: Ina Son in Gaji El-Rufai, Zan Cigaba Daga Inda Ya Tsaya, Kwamishinan Jihar Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Kamar yadda ya bayyana:

“Na yi wannan wallafar ne don sanar da niyyata ta fara kamfen din neman kujerar gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023 da ke karatowa.”

Ya ce zai dasa daga inda El-Rufai ya tsaya

Yayin yaba wa gwamnan akan ba shi damar yin aiki da gwamnatin sa, The Punch ta ruwaito yadda tsohon shugaban ma’aikatan jihar ya ci gaba da cewa:

“Tsawon shekaru bakwai da suka gabata, na samu damar yin aiki tare da gwamnan mu, uba kuma shugaba Nasir El-Rufai yayin kokarinsa na gyara jihar mu.
“Tun da aka kafa Jihar Kaduna a tarihi, ba a taba samun gyara irin wanda aka yi daga shekarar 2015 zuwa yanzu ba. Yayin da na samu damar yin ayyuka a manyan mukamai, daga shugaban ma’aikatan jihar zuwa kwamishina; na samu damar yin aiki tukuru don ciyar da jihar gaba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Uba Sani ya bayyana kudurinsa na neman kujerar gwamnan Kaduna a APC a 2023

“Ina da yakini akan cewa zan iya yin aiki kwarai tare da samar ci gaba mara misaltuwa sannan in dasa daga inda Malam Nasir El-Rufai ya tsaya.”

Ya kara da cewa saboda gogewar sa, zai tabbatar ya yi aiki komai wuya komai rintsi don tallafa wa Jihar Kaduna.

Hakan yasa ya ce yana so a ba shi damar yin aiki kwatankwacin wanda mutanen Kaduna suka gani a shekaru 7 da suka gabata.

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Akwai Yiwuwar Mace Ce Za Ta Zama Gwamnan Kaduna A 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel