Tsohon gwamna Kwankwaso: Duk ranar da na fice daga PDP, daga nan ta zama gawa

Tsohon gwamna Kwankwaso: Duk ranar da na fice daga PDP, daga nan ta zama gawa

  • Jam'iyyar PDP za ta ruguje idan tsohon gwamnan Kano Rabi'u Kwankwaso ya koma jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP)
  • Wannan shi ne hasashen da shi Sanata Kwankwaso ya yi a wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin, 14 ga watan Maris
  • Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana cewa idan ya koma jam’iyyar NNPP, PDP za ta bar matsayin jam’iyyar siyasa ta biyu a Najeriya

Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, ya yi alfaharin cewa idan ya fice daga jam’iyyar PDP, za ta ruguje.

Da yake magana yayin wata tattaunawa da Channels Tv, jigon na PDP kuma mai fada a ji a Arewacin kasar ya nuna shakku kan cancantar shugabancin jam’iyyar kuma ya yi hasashen cewa babu abin da zai same shi idan ya koma jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Saraki ya yi magana a kan ficewar Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP

Hasashen karshen PDP daga Kwankwaso
Tsohon gwamna Kwankwaso: Duk ranar da na fice daga PDP, daga nan ta zama gawa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Duk da cewa Kwankwaso ya bayyana cewa har yanzu bai sauya sheka zuwa jam’iyyar ta NNPP ba, ya ce kungiyarsa ta siyasa, National Movement, tuni ta shiga NNPP.

Ya bayyana tabbacin cewa jam’iyyar NNPP za ta fi PDP karfi kuma za ta zama ta biyu idan ya shiga inuwarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Manyan 'yan PDP basu dauke ni da muhammanci ba, inji Kwankwaso

Akan dalilin da ya sa yake shirin ficewa daga jam’iyyar PDP, Kwankwaso ya koka da yadda wasu masu rike da madafun iko a PDP ke daukarsa a ba komai ba suna mayar da ikonsa zuwa ga rauni.

Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa an zage shi a taron da ya gabata a yankin Arewa maso Yamma inda a cewarsa aikin zaben wanda aka zaba a matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa an baiwa wani ne.

Kara karanta wannan

Rudani kan batun shiga NNPP: Har yanzu ni dan PDP ne, Kwankwaso ya yi bayani

Ya shaidawa Channels Tv cewa:

“Ya kamata in kasance daya daga cikin manyan mutane a jam’iyya kamar PDP.
"Saboda dalilai da yawa da ke bayyane kuma daga abin da muke gani, abin ya yi kama da mutane da yawa suna sauya ikona zuwa rauni kuma hakan ba zai yiwu ba.
“Dubi abin da ya faru a yankin Arewa maso Yamma a lokacin taron gangami, daga abubuwan da aka kai Kano, mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar ya kamata a ba ni in zabi wani.
"Kamar yadda aka yi a Katsina, (Tsohon Gwamna Ibrahim) Shema ne ya zabi abin da aka ware masa, a Kaduna (Tsohon Gwamna Ahmed) Makarfi ya yi haka, a Jigawa (Tsohon Gwamna) Sule Lamido ya yi haka, a Kebbi Kabiru Turaki ya yi haka, a Sakkwato (Gwamna Aminu) Tambuwal ya yi haka."

Kwankwaso muke bi ba jam'iyya ba

Legit.ng Hausa ta tattauna da wani dan a-mutum Kwankwaso, kuma dan Kwankwasiya, inda ya shaida cewa, da yawansu su 'yan Kwankwasiya ba jam'iyyar siyasa suke bi ba.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP

Alhaji Mu'azu Adamu Idris ya bayyana cewa, shi dai ba mazaunin Kano bane, amma yana kaunar tafiyar Kwankwaso saboda wasu halaye na sanatan.

Ya bayyana cewa:

"Idan Kwankwasi zai fito takarar shugaban kasa, to mu 'yan Kwankwasiya za mu zabe shi, saboda kyawunsa muke dubawa ba jam'iyya ba.
"'Yan siyasa nawa ne ke kaura daga jam'iyya saboda su samu kujerun siyasa? To a bangarenmu, mu kawai dai Kwankwason, ba komai ba.
"Mun yarda dashi, mun kuma amince da shawarin da zai dauka na sauya sheka ko zama a PDP, duk daya ne. Amma mu mabiyansa ya kamata a sani muna da yawa."

Saraki ya yi magana a kan ficewar Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi magana a game da rahotanni da suke yawo a kan sauya-shekar Rabiu Musa Kwankwaso.

Dr. Abubakar Bukola Saraki ya yi magana ne jim kadan bayan an ji Rabiu Musa Kwankwaso ya fito yana cewa har zuwa yau shi ‘dan jam’iyyar PDP ne.

Kara karanta wannan

An tunawa ‘Yar Abiola abin da ta fada a 2018 a kan APC yayin da ta shirya tsayawa takara

Sanata Kwankwaso ya nuna ya ba jam’iyyar hamayyar damar tayi zawarcinsa, a sakamakon sabanin da aka samu har ta kai ya kafa kungiyar TNM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel