Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP

Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP

  • Wasu makusantan Sanata Rabiu Kwankwaso sun ziyarci Ibrahim Shekarau a gidansa domin sa labule
  • An tattaro cewa yan siyasar na kokarin ganin sun lallaba Shekarau ya dawo PDP yayin da ubangidan nasu ke shirin komawa NNPP
  • Yan siyasar dai sun sha alwashin ba za su bi ubangidan nasu zuwa sabuwar jam'iyyar da yake shirin komawa ba gabannin 2023

Abuja - Siyasar Kano ta dauki sabon salo yayin da wasu manyan hadiman tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso suka ziyarci Ibrahim Shekarau a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata.

Majiyoyi sun bayyana cewa bakin na kokarin shawo kan babban abokin adawar ubangidan nasu domin ya dawo jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya bari gabannin zaben 2019 saboda dawowar Kwankwaso jam’iyyar, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

APC ta gamu da gagarumin cikas a wata jihar kudu yayin da kansiloli 5 suka fice, sun koma PDP

Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP
Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Shekarau ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne bayan PDP ta mika shugabancinta a jihar ga Kwankwaso, wanda ya kasance dan jam’iyyar tun bayan kafata a 1998, har zuwa lokacin da ya koma sabuwar APC a 2014.

Yanzu, Kwankwaso na shirin sake sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Shima Shekarau wanda yake sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya a yanzu, hankalinsa bai kwanta da APC mai mulki ba a yanzu. Basa ga maciji da Gwamna Abdullahi Ganduje kan shugabancin jam’iyyar a jihar.

A ranar Alhamis, shugaban ma’aikatan tsohon gwamna Kwankwaso, Adamu Dangwani, tare da tsohon dan majalisar tarayya, Danburam Nuhu, tsohon kwamishina, Yusuf Danbatta da Hadiza Adado; wadanda suka kasance makusantan Kwankwaso, sun ziyarci Shekarau a Abuja kan sauya yanayin siyasa a jihar.

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

An tattaro cewa yan siyasar sun sha alwashin kin bin Kwankwaso zuwa NNPP.

Mai magana da yawon Shekarau ya tabbatar da ziyarar

Kakakin Shekarau, Sule Ya’u, ya tabbatar da ziyarar da yan siyasar suka kaiwa ubangidan nasa.

Ya fada ma manema labarai cewa:

“Dangwani da wasu mambobin PDP bangaren Kwankwasiyya karkashin jagorancin tsohon dan majalisa Hon Danburan, sun ziyarci Sanata Ibrahim Shekarau a gidansa na Abuja domin tattaunawa.”

Ya’u bai bayyana dalilin ziyarar ba. Sai dai masu hasashe sun ce hakan baya rasa nasaba da alwashin da wasu yan Kwankwasiyya suka dauka na kin sake binsa wajen barin PDP.

Majiyoyi sun ce yan siyasar na PDP na kokarin lallaba Shekarau ne domin ya sake dawowa PDP tunda Kwankwaso zai barta zuwa NNPP.

Babu wani aibu don mutum ya sauya sheka a siyasa - Kwankwaso

A gefe guda, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa shi bai ga wani aibu ba don yan siyasa sun sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata, cewa hakan wani tsari ne na siyasa.

Kara karanta wannan

An tunawa ‘Yar Abiola abin da ta fada a 2018 a kan APC yayin da ta shirya tsayawa takara

Kwankwaso ya bayyana cewa akwai hikima sosai idan dan siyasa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya domin gwada farin jininsa da kuma karbuwarsa a cikin mutane.

Dan siyasan ya bayyana hakan ne a Kano, a ranar Lahadi, 6 ga watan Maris, yayin wata ganawa da yan Kwankwasiyya da kuma jiga-jigan PDP a jihar a gidansa da ke Miller Road, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel