Rudani kan batun shiga NNPP: Har yanzu ni dan PDP ne, Kwankwaso ya yi bayani

Rudani kan batun shiga NNPP: Har yanzu ni dan PDP ne, Kwankwaso ya yi bayani

  • Yayin da 'yan Kwankwasiyya suka fara shirin tsundumawa jam'iyyar NNPP, Kwankwaso ya ce har yanzu shi dan PDP ne
  • Ya bayyana haka ne a yayin wara hira da kafar labarai, inda ya ce akwai shirye-shirye da dama game da tafiyar siyasarsa
  • Tuni dai wasu masu sharhi sun fara bayyana cewa, karshen PDP zai zo a yankin Arewa matukar Kwankwaso ya bar PDP

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce har yanzu shi dan jam’iyyar PDP ne, duk da kuwa ya tabbatar da tattaunawa tsakaninsa da jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP a kwanakin nan).

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta BBC, inda ya kara da cewa kungiyar siyasa da aka kaddamar kwanan nan; ‘National Movement’ ce ta haifi NNPP.

Kara karanta wannan

Saraki ya yi magana a kan ficewar Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP

Batun Kwankwaso da NNPC da PDP
Rudani kan batun shiga NNPC: Har yanzu ni dan PDP, Kwankwaso ya yi bayani | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa a watan Fabrairun 2022, Kwankwaso ya halarci cibiyar taron kasa da ke Abuja domin kaddamar da kungiyar TNM, tare da wasu manyan ‘yan siyasar kasar nan.

An ruwaito Kwankwaso na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

''A yanzu maganar da ake yi ina cikin jam'iyyar PDP, tun wancan lokacin mun fara abin hawa-hawa."

Hakazalika, Kwankwaso ya bayyana irin shirin da ke kasa na tafiyar da harkokin siyasarsa, ya kara da cewa:

"Abu na farko da muka fara yi shi ne ja baya daga tsarinta, tunanin wasu masu hankali za su zo a zauna a fada musu abin da ya dame mu amma jam'iyya ba ta yi ba, muka shiga kungiya nan ma ba a yi komai ba, to gamu a matakin jam'iyya.
"Har yanzu da na ke magana da kai muna tsakanin kungiya da jam'iyya sannan ban fita daga cikin jam'iyyar PDP ba, kuma wannan kungiya ta hade ne da jam'iyyar NNPP."

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP

Da yake bayyana yiwuwar barinsa jam'iyyar PDP, ya shaidawa BBC cewa, idan lokaci yayi manema labarai ne mutanen farko da zai fara sanar dasu ficewarsa.

A kalamansa:

"Duk ranar da zan bar PDP ku ne na farko da za ku sani saboda abubuwan ne a tsare su ke mu na komai cikin tsanaki.''

A kwanan nan ne wasu daga cikin masoya Kwankwaso ke ziyartar manyan ‘yan siyasa domin tuntubar Shekarau, Sule Lamido da Atiku Abubakar.

Karshen PDP a Kano da Arewa kenan: Shugaban PDP ya damu da ficewar Kwankwaso

A wani labarin, da alamu dai ficewar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Kwankwaso daga PDP ka iya haifar da damuwa tsakanin 'ya'yan jam'iyyar PDP a jihar.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, Shehu Sagagi, ya ce barin Kwankwaso ya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar NNPP babban kuskure ne.

Kara karanta wannan

Katsina: Yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota, sun kashe fasinjoji 5

Sagagi ya kuma yi kira ga manyan masu ruwa da tsaki na PDP da su tuntubi Kwankwaso domin jin matsalarsa da kuma neman hanyoyin magance su tun kafin lokaci ya kure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel