Saraki ya yi magana a kan ficewar Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP

Saraki ya yi magana a kan ficewar Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya tofa baki a game da siyasar PDP a jihar Kano
  • Dr. Bukola Saraki ya bayyana farin cikinsa da jin cewa Sanata Rabiu Kwankwaso yana nan a PDP
  • Rabiu Kwankwaso ya tabbatar da cewa har zuwa yanzu da ake magana shi ‘dan jam’iyyar PDP ne

Abuja - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi magana a game da rahotanni da suke yawo a kan sauya-shekar Rabiu Musa Kwankwaso.

Dr. Abubakar Bukola Saraki ya yi magana ne jim kadan bayan an ji Rabiu Musa Kwankwaso ya fito yana cewa har zuwa yau shi ‘dan jam’iyyar PDP ne.

Sanata Kwankwaso ya nuna ya ba jam’iyyar hamayyar damar tayi zawarcinsa, a sakamakon sabanin da aka samu har ta kai ya kafa kungiyar TNM.

Kara karanta wannan

Rudani kan batun shiga NNPP: Har yanzu ni dan PDP ne, Kwankwaso ya yi bayani

Da yake bayani a shafinsa na Twitter, tsohon shugaban majalisar dattawan na Najeriya ya bayyana farin cikinsa da jin Kwankwaso bai bar PDP ba.

Tsohon gwamnan na jihar Kwara yake cewa wasu daga cikin dakarun tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar PDP a Kano sun ziyarce shi a gidansa da ke Abuja.

Saraki da Rabiu Kwankwaso
Dr. Bukola Saraki da Sanata Rabiu Kwankwaso Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kusoshin Kwankwasiyya sun ziyarci Saraki

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wadanda suka kai wa Bukola Saraki ziyara har gida daga cikin jagororin Kwankwasiyya sun hada da Dr. Yunusa Dangwani.

Haka zalika an ga su Jamilu Danbatta, Abubakar Nuhu Danburam da Yunusa Dangwani a gidan babban 'dan siyasar a ziyarar da suke kai wa manyan PDP.

“Na yi farin cikin karanta labari cewa abokina, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi karin-haske a game da jam’iyyar da yake ciki.”
“Wannan shi ne abin da ya kamata.”

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Makusantan Kwankwaso sun lallaba sun gana da Shekarau, suna kokarin sake jawo shi PDP

“Bayan tattaunawa da wasu da-dama daga cikin jagorori da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar Kano da suka kai mani ziyara a gida na a karshen makon da ya wuce a garin Abuja…
…Ina da cikakken tabbacin cewa Sanata Kwankwaso da mutanen da ya kafa za su zauna a jam’iyyar PDP domin a ceto Najeriya, kuma a kawo gyara.”

- Abubakar Bukola Saraki

Kwankwaso zai yi takara?

Dazu mun kawo maku ‘yan siyasan da za su iya bayyana shirin takarar shugaban kasa nan da kwanaki masu zuwa. Daga ciki har da Sanata Rabiu Kwankwaso.

Bisa dukkan alamu tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai bayyana niyyar takarar shugaban kasa a zaben 2023 da zarar ya shiga NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel