Kano, Kaduna, Borno Da Wasu Jihohi 18 Da Ka Iya Fuskantar Yunwa, Rahoto

Kano, Kaduna, Borno Da Wasu Jihohi 18 Da Ka Iya Fuskantar Yunwa, Rahoto

  • Rahoton watanni ukun farkon shekarar 2022 na Cadre Harmonisé (CH) ya nuna cewa akwai yiwuwar mutane miliyan 19.4 ciki har da ‘yan gudun hijira daga jihohi 20 da kuma Abuja su fuskanci yunwa tsakanin watan Yuni da Augustan 2022
  • Rahoton ya nuna cewa yanzu haka kusan mutane miliyan 14.4 ciki har da ‘yan gudun hijira 385,000 da ke jihohi 20 da Abuja suna fama da yunwa kuma alamu suna nuna cewa zasu ci gaba da zama a haka har watan Mayun 2022
  • Binciken Cadre Harmonisé (CH) wani salo ne na nazari akan yunwa a yankin Sahel da kasashen yankin Afirka ta yamma ciki har da Najeriya, kuma an gabatar da rahoton ne jiya a Abuja

Abuja - Rahoton Cadre Harmonisé na watanni ukun farkon shekarar 2022, ya nuna cewa kusan mutane miliyan 19.4 ciki har da ‘yan gudun hijira 416,000 da ke jihohi 20 da kuma babban birnin tarayya, Abuja za su iya fuskantar yunwa tsakanin watan Yuni da Augustan shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Iyalan Abacha Sun Nemi Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Biya Su N11.7bn Da N200m Domin Rushe Otel

Rahoton ya nuna cewa kusan mutane miliyan 14.4 ciki har da ‘yan gudun hijira 385,000 da ke jihohi 20 da kuma Abuja yanzu haka suna cikin yunwa, kuma hakan zai ci gaba har watan Mayun 2022, Daily Trust ta rauwaito.

Kano, Kaduna, Borno Da Wasu Jihohi 18 Da Ka Iya Fuskantar Yunwa, Rahoto
Kano, Kaduna, Borno Da Wasu Jihohi 18 Da Ka Iya Fuskantar Karancin Abinci, Rahoto. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Binciken Cadre Harmonisé (CH) wani salo ne na sanin yadda mizanin yunwa da rashin abinci a yankin Sahel 17 da kasashen Afirka ta Yamma ciki har da Najeriya.

Kungiyoyi da dama sun dunkule wurin kawo mafita ga matsaloli musamman na yunwa a Najeriya

A Najeriya, ma’aikatar noma da bunkasa karkara, kungiyar abinci da noma ta majalisar dinkin duniya (FAO), shirin samar da abinci na duniya (WFP) da sauran kusoshi sun hada kai wurin kawo mafita ga wannan matsalar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito yadda rahoton ya kunshi jihohi 21 da ke Najeriya kamar: Abia, Adamawa, Bauchi, Benue, Borno, Cross-River, Edo, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Legas, Neja, Filato, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da Abuja.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, rayuka sun salwanta

Rahoton ya nuna rashin tsaro, musamman a arewa maso gabas, tsadar kayan masarufi, tsadar kayan abinci da kuma tabarbarewar tattalin arzikin saboda annobar COVID-19 su ne suka janyo yunwar.

Binciken yana taimakawa wurin sanin hanyar bullo wa yunwa a kasa kafin ta riski jama’a

Yayin gabatar da rahoton, jiya a Abuja, wakilin FAO a Najeriya da kuma ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta yamma (ECOWAS), Mr Fred Kafeero ya ce akwai bukatar a kawo gyara a harkokin samar da abinci duba da yadda ake sa ran 2030 za ta kasance.

Kafeero, ya samu wakilcin Farfesa Salisu Mohammed wanda ya yi kira ga gwamnati akan samar da mafita ga rahoton CH din wurin shirye-shiryen kasa, ta hanyar kawo salon da zai taimaka wurin wadatar abinci a kasa.

A bangaren sa, sakataren ma’aikatar noma da bunkasa karkara, Dr Ernest Umakhihe, ya ce binciken CH yana da muhimmanci don sanin yadda za a bullo wa yunwa a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel