Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

  • Ogbonnaya Onu, Ministan Kimiyya da Fasaha ya ce Nigeria ta yi watsi da irin halayen mazan jiya da suka kafa kasar
  • Onu ya ce wannan sauka daga turbar da mazan jiya suka dora kasar yasa ta gaza cimma nasarar shige jerin kasashe da suka bunkasa a duniya
  • Ministan ya yi wannan jawabin ne a birnin tarayya Abuja wurin karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya)

Abuja - Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen jihohin Najeriya 12 da UK ta shawarci 'yan kasar ta da su kiyaya

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata shiga jerin kasashen da suka bunkasa ba, Ministan Buhari
Minista Kimiyya da Fasahar Nigeria, Ogbonnaya Onu. Hoto: Daily Trust

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

A cewarsa:

"Admiral Ndubuisi Kanu yana da wadannan halayen, halayen gaskiya, aiki tukuru, halaye na gari da zama misali ga saura. Wadannan ne irin halayen da muke bukata mu koya wa yaran mu domin su daura Nigeria kan turbar cigaban da dukkan mu muke fatan gani."

Onu ya cigaba da cewa ya kamata a rubuta tarihin tsohon gwamnan na Legas da Imo domin matasa su san cewa:

"Halaye masu kyau na da amfani, bin dokoki na da amfani kuma riko da gaskiya na da matukar tasiri."

Tsohon babban hafsan tsaro na kasa, Laftanat Janar Azubuike Iherijirika (mai ritaya) ya ce Ndubuisi ya yi rayuwa ta rashin girman kai da mutunta al'umma.

Kara karanta wannan

Ku ba 'yan bindiga hadin kai don tsira da rayukanku, shawarin 'yan sanda ga 'yan Najeriya

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel