Iyalan Abacha Sun Nemi Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Biya Su N11.7bn Da N200m Domin Rushe Otel

Iyalan Abacha Sun Nemi Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Biya Su N11.7bn Da N200m Domin Rushe Otel

  • Iyalan Janar Sani Abacha, tsohon shugaban mulkin soja ta Najeriya sun bukaci kotun jihar Kaduna ta umurci Gwamna El-Rufai ya biya su N11.7bn da N200m
  • Suna neman wannan kudin ne a matsayin diyya kan ikirarin da suka yi na cewa El-Rufai da wasu jami'an gwamnatinsa sun kutsa musu otel sun kuma rushe ginin
  • Har wa yau, iyalan na tsohon shugaban sojan sun nemi kotun ta hana wa El-Rufai, wakilansa da kowa siyar da filin ko mika shi ga wani ko wani abu makamancin hakan

Kaduna - Iyalan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Sani Abacha ta bakin lauyansu na Durbar Hotel Plc, Kaduna, Dr Reuben Atabo, SAN, suna neman a biya su diyyar N11,509,399,355.44 kan rushe hotel dinsu da gwamnatin Nasir El-Rufai ta yi a Janairun 2020.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya bayar da gudunmawar miliyan N30 ga iyalan yan-sa-kai da aka kashe a Kebbi

Cikin karar da iyalan na Abacha suka shigar mai kwanan watan 10 ga watan Maris din 2022, a babban kotun jihar, sun kuma nemi a biya su N200 miliyan saboda musu kutse a gida/fili, rahoton Vanguard.

Iyalan Abacha Sun Nemi Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Biya Su N11.7bn Da N200m Domin Rushe Otel
Iyalan Abacha Sun Nemi Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Biya Su N11.7bn Da N200m Domin Rushe Durbar Hotel. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Lauyan Iyalan Abacha ya nemi a hana kowa taba filin ko kuma sayar da shi

Dr Atabo ya bukaci babban kotun jihar da Mai shari'a Hannatu Balogun ke jagoranta ta dakatar da duk wasu matakai da wanda aka yi karar suka dauka kawo yanzu da ya danganci gininsu da ke Lamba 1 Independence Way Kaduna na mika shi ga wani daban.

Atabo, SAN, ya mika takarda ga kotun na neman a hana wanda aka yi kara ko wakilansa daga taba filin da ke Lamba 1 Independence Way Kaduna, Jihar Kaduna, mai fadin hecta 5.578 da lamba 17789, ko mika ta ga wani ko sayarwa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Kotu ta dage sauraron shari'ar

Mai Shari'a Balogun ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Maris na 2020 wato Alhamis kamar yadda ya zo a rahoton Vanguard.

El-Rufai ya fusata ABU Zaria, ASUU ta bukaci a soke Digirorin da aka ba shi a 1980

A wani labarin, Kungiyar malaman jami’a na reshen jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta yi kira ga shugabannin jami’ar da su karbe digirorin Nasir El-Rufai.

Rahoto ya fito daga jaridar Abusites cewa kungiyar ASUU ta cin ma matsaya cewa a raba Malam Nasir El-Rufai da shaidar karatun da ya samu a jami’ar.

Hakan na zuwa ne bayan sabanin da aka samu tsakanin mai girma gwamnan na jihar Kaduna da shugabannin jami’ar ABU Zaria game da batun wani fili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel