Za Mu Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga Da Masu Kai Musu Bayanan Sirri, Tambuwal Ya Ba Mazauna Sokoto Tabbaci

Za Mu Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga Da Masu Kai Musu Bayanan Sirri, Tambuwal Ya Ba Mazauna Sokoto Tabbaci

  • Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar wa mazauna Jihar Sokoto cewa gwamnatinsa zata kawo karshen ‘yan bindiga
  • A ranar Laraba ya ja kunnen masu hada kai da su wurin basu bayanan sirri inda yace su yi gaggawar dainawa ko kuma su fuskanci fushin hukuma
  • A takardar da kakakinsa, Muhammad Bello ya saki, ya bayyana yadda gwamnan yace gwamnatinsa a shirye take ta taimaka wa jami’an tsaro wurin cimma wannan kudirin

Sokoto - A ranar Laraba, Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar wa mazauna jiharsa cewa gwamnatinsa ya shirya tsaf wurin kawo karshen ‘yan bindiga da masu kai musu bayanan sirri a fadin jihar.

Har ila yau ya ja kunnen masu hada kai da su wurin tayar da hankali a jihar ko kuma su fuskanci fushin hukuma, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Allah ya tabbatar mun' Gwamnan PDP a Arewa ya fadi kujerar da zai fafata a zaben 2023

Za Mu Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga Da Masu Kai Musu Bayanan Sirri, Tambuwal Ya Ba Mazauna Sokoto Tabbaci
Za Mu Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga Da Masu Kai Musu Bayanan Sirri, Tambuwal Ga Mazauna Sokoto. Hoto: The Punch
Asali: Depositphotos

Tambuwal ya bayar da wannan tabbacin ne da daren Talata inda ya nuna takaicin sa akan yadda ‘yan bindiga da masu kai musu bayanai suka addabi kauyen Sabon Garin Liman da ke karamar hukumar Wurno a jihar.

Ya ce a shirye gwamnatin sa take da ta kawo karshen ta’addanci a jihar

A wata takarda wacce kakakinsa, Muhammad Bello ya saki kamar yadda The Punch ta ruwaito, ya yanko daidai inda gwamnan ya ce gwamnatinsa tana iyakar kokarin ta na tallafa wa jami’an tsaro wurin kawo karshen ‘yan bindiga.

Ya ce gwamnatin sa ta san abubuwan da ke faruwa a kauyen wanda ‘yan bindigan ciki da wajen kasar suke shiga suke cin karen su babu babbaka.

Kamar yadda ya ce:

“Bana cikin jihar. Na bar Sokoto jiya amma saboda labarin ‘yan bindiga da na ji yasa na fito da misalin karfe 1 na dare saboda tsabar damuwar da nayi da abubuwan da ke faruwa a dajin Gundumi a Jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan APC a arewa za su siyawa Umahi fam din takara

“Mun san akwai masu kai musu labari a kauye. Zamu tabbatar mun binciko su sannan mu tabbatar doka ta yi aiki a kan su.”

Ya yi kira ga mutanen Sokoto masu bin doka akan su hada kai da shugabannin kauye, shugabanni na gwamnati da jami’an tsaron da aka tura yankunan su don kawo garanbawul akan matsalar tsaro.

Ya ce ba za su bari lamarin da ya auku a Kebbi ya faru a jiharsa ba

Ya jajanta wa mutane akan abubuwan da ke faruwa na hare-hare.

A cewarsa, ba zasu bari lamarin da ya auku a Jihar Kebbi wanda ‘yan bindiga suka halaka ‘Yan Sa Kai akalla 60 a ranar Lahadi da yamma ya maimaita kansa a Sokoto ba.

Hakan yasa yace wajibi ne su hada kai wurin ganin an samu ci gaba a jihar, maimakon ci baya.

Ya yi wa wadanda lamarin ya ritsa da su addu’o’i inda ya ce:

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

“Muna fatan Ubangiji ya gafarta wa wadanda suka mutu sannan ya ba wadanda suka ji ciwo lafiya ya kuma kiyaye gaba.”

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel