Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

  • Miji da Mata sun yi rashin rayukansu a garin Jos sakamakon tashin wuta a inda sukayi ajiyan jarkokin mai
  • Gobarar ta lakumesu kurmus ta yadda ko gane gawawwakinsu an gaza yi, cewar shugban hukumar Fire
  • Mai magana da yawun Buhari ya yi kira ga yan Najeriya su cigaba da hakuri kan wahalan rashin man da ake fama da shi

Plateau - Wahalar mai da ake fama da shi a fadin tarayya ta yi sanadin mutuwar wani dan kasuwar bayan fagge, wadanda akafi sani da 'yan bunburutu' da matarsa a garin Jos.

Miji da matan sun mutu ne ranar Alhamis yayinda wuta ta tashi cikin dakin girkinsu inda mijin mai suna Gideon Pam yayi ajiyan jarkokin man fetur a unguwar Zawan, karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Rashin mai da rashin wuta: Ku cigaba da juriya, ai ba mulkin Buhari aka fara rashin ba: Femi Adesina

Man fetur
Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida Hoto: NAN
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata makwabciyarsu, Miss Shantel Alphonsus, ta bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) cewa Gideon na sayar da mai ta bayan fagge a Zawan.

Tace:

"Da safe aka kira shi cewa ya zo ya karbi mai daga gidan mai, sai ya koma gida ya debo jarkoki."
"Yayinda yake kokarin juye feturin dake cikin jarkokin, kawai sai wuta ya tashi cikin Kitchen din da ya ajiye jarkokin."
"Matarsa Mercy ta shiga kitchen din ceton mijinta amma wutar ta ritsa da ita."

Miss Shantel ta bayyana cewa basu dade da haihuwan sabon jariri ba.

Diraktan hukumar kashe gobara na jihar Plateau, Caled Polit, ya tabbatar da lamarin kuma yayi Alla-wadai kan yadda wutar ta babbakasu kafin jami'an kwana-kwana su iso.

Ku kwantar da hankulanku, muna da litan mai 1.7bn: Shugaban NNPC ga yan Najeriya

Kara karanta wannan

Mamayar Rasha: Mutane miliyan 1 sun yi gudun hijira a Ukraine cikin mako 1, UNHCR

Kamfanin man Najeriya NNPC ya yi kira ga yan Najeriya su daina tada hankulansu suna ajiyan man fetur saboda akwai isasshen mai a ajiye da za'a fitar.

Dirakta Manaja na NNPC, Mele Kyari, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Abuja ranar Laraba bayan ganawarsa da kungiyar ma'aikatan man fetur da kungiyar direbobin tankan mai (PTD).

Sauran kungiyoyin dake hallare a ganawar sun hada da kungiyar yan kasuwar mai na Depot, DAPMAN, da kungiyar manyan yan kasuwan mai MOMAN.

Asali: Legit.ng

Online view pixel