Jerin sunayen sabbin kwamishinonin ICPC 5 da majalisar dattawa ta dabbatar da su

Jerin sunayen sabbin kwamishinonin ICPC 5 da majalisar dattawa ta dabbatar da su

  • Majalisar dattawa ta tabbatar da sabbin kwamishinonin hukumar ICPC biyar bayan shugaban kasa Buhari ya zabe su
  • Majalisar ta tabbatar da kwamishinonin ne a zamanta na yau Laraba, 9 ga watan Maris
  • Hakan ya biyo bayan samun rahoton kwamitin majalisar wanda ya tantancesu karkashin jagorancin Sanata Suleiman Abdu Kwari

Abuja - Majalisar dattawa ta tabbatar da zababbun kwamishinonin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.

Majalisar ta tabbatar da su ne a ranar Laraba, 9 ga watan Maris, bayan duba rahoton kwamitin majalisar kan yaki da rashawa da laifukan da suka shafi kudi, jaridar Punch ta rahoto.

Jerin sunayen sabbin kwamishinonin ICPC 5 da majalisar dattawa ta dabbatar da su
Jerin sunayen sabbin kwamishinonin ICPC 5 da majalisar dattawa ta dabbatar da su Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Sabbin kwamishinonin da aka tabbatar sun hada da:

1. Sanata Anthony Agbo

Kara karanta wannan

2023: Kwankwasiyya da 'Yan kungiyar TMN za su narke a cikin jam'iyyar NNPP

2. Anne Otelafu Odey

3. Alhaji Goni Ali Gujba

4. Dr. Louis Solomon Mandama

5. Olugbenga Adeyanju AIG (mai ritaya).

Buhari ya janye suna daya sannan ya maye gurbinsa da wani

A jawabinsa, shugaban kwamitin, Sanata Suleiman Abdu Kwari, ya tuna cewa shugaba Buhari ya janye sunan daya daga cikin zababbun kwamishinonin, Misis Mojisola Yaya-Kolade sannan ya maye gurbinta da Olugbenga Adeyanju AIG (mai ritaya), wanda kwamitin ya tantance.

Ya bayyana cewa zababbun kwamishinonin sun bayar da amsa yadda ya kamata yayin amsa tambayoyin kwamitin kan yadda za su cika aikin hukumar.

Ya kara da cewa, bayan bincikar takardunsu, kwamitin ya gamsu da cewa wadanda aka zaba suna da kwarewa, mutunci kuma za su iya sauke ayyukan da aka zabe su suyi."

Ya kuma bayyana cewa, babu wani rahoto na tsaro ko korafe-korafe da aka yi kan wani daga cikin wadanda aka nada.

Cin Hanci: Shugaban EFCC ya goyi bayan kalaman Obasanjo kan masu neman gaje Buhari a 2023

Kara karanta wannan

Kafin Ramadan zamu maida Magidanta 500 da tallafin N100,000 ga kowa Insha Allahu, Zulum

A wani labarin, Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya bayyana goyon bayansa ga kalaman tsohon shugaban ƙasa, Chief Olusegun Obasanjo.

Daily Trust ta rahoto Cewa Obasanjo ya yi ikirarin cewa duk waɗan nan yan siyasan dake son ɗare wa kujerar Buhari a 2023, suna da tabon da ya kamata ace suna ɗaure a kurkuku.

Bawa, wanda ya yi hira da yan Jarida a Legas, ya ce hukumarsa ba ta da ikon hana yan siyasa neman takara duk da suna gaban Kotu, tun da akwai yuwuwar ba su da laifi har sai an tabbatar da sun aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel