2023: Kwankwasiyya da 'Yan kungiyar TMN za su narke a cikin jam'iyyar NNPP

2023: Kwankwasiyya da 'Yan kungiyar TMN za su narke a cikin jam'iyyar NNPP

A cikin kwanakin nan tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya kafa wata kungiyar siyasa, TNM, wanda a daren Litinin suka koma jam'iyyar NNPP.

NNPP tana daya daga cikin jam'iyyu masu rijista a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito hakan.

2023: Kwankwasiyya da 'Yan kungiyar TMN za su narke a cikin jam'iyyar NNPP
2023: Kwankwasiyya da 'Yan kungiyar TMN za su narke a cikin jam'iyyar NNPP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Yayin zantawa bayan taron awa bakwai a Abuja, shugaban jam'iyyar TNM na rikon kwarya, AVM John Chris Ifeimeji (mai ritaya), ya ce, kungiyar ta yanke shawarar shigar da NNPP don ceto kasar daga mulkin kama karya da jam'iyyar mai mulki ke yi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an nada Ifeimeji a matsayin shugaban kwamitin kula da Jam'iyyar NNPP.

Ya ambaci sanata Suleiman Hunkuyi na jihar Kaduna; tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung; fitaccen mai caccaka a arewa, Buba Galadima; da sauran fitattun 'yan Najeriya a matsayin masu kula da kwamitin.

Kara karanta wannan

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran mambobin kwamitin rukon kwaryar sun hada da; Dr Boniface Aniebonam a matsayin shugaban kwamitin, kwamitin yar daddu (BoT); Sanata Hunkuyi, mataimakin shugaban kwamitin; da Hon. Oladipo Olayoku, sakataran jam'iyya na ksa; Manji Gilbert Agho, sakataran watsa labarai na kasa; da ferfesa Rufa'i Ahmed Alkali, sakataran shirye-shirye na kasa da dai sauran su.

A cewarsa, kungiyar ta samu karbuwa a fadin kasar, tun lokacin da aka bude ta a wancan watan da ya gabata, yayin da mutane da dama da kungiyoyi suke tururuwar zuwa wurin sakataran TNM don a san dasu gami da shiga jam'iyyar.

"Saboda haka, TNM tayi maja da NNPP. Mambobin TNM sun shiga gami da amincewa da yin maja da NNPP, saboda suna matukar kamanceceniya da juna, dokoki da ka'idojin su sun yi matukar zuwa iri daya," a cewar Ifeimeji.

Kara karanta wannan

Sai irin su Buhari: Osinbajo ya bayyana wanda iya zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Kwankwaso, tsohon ministan Buhari: Jerin yan siyasar da suka kafa sabuwar kungiyar siyasa

A wani labari na daban, gabannin babban zaben 2023, an kafa wata sabuwar kungiyar siyasa da ke neman karbe mulki daga hannun jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP).

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ne ya sanar da kafa sabuwar kungiyar siyasar mai suna ‘The National Movement (TNM)’ a babban cibiyar taro ta kasa da ke Abuja, a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel