Sai irin su Buhari: Osinbajo ya bayyana wanda zai iya magance matsalar tsaro a Najeriya

Sai irin su Buhari: Osinbajo ya bayyana wanda zai iya magance matsalar tsaro a Najeriya

  • Mataimakin a ziyarar ban girma da ya kai jihar Delta ya bayyana cewa irin shugaba Buhari ne kadai zai iya magance matsalar rashin tsaro a Najeriya
  • Osinbajo ya kuma bayyana cewa, hadin gwiwar gwamnati da sarakunan gargajiya a kasar zai kara taimakawa wajen yaki da ta’addanci
  • Idan baku manta ba, shugaba Buhari ya shilla kasar Burtaniya domin duba lafiyarsa, ya bar Najeriya a hannun mataimakinsa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa domin tunkarar kalubalen tsaro a Najeriya yadda ya kamata, kasar na bukatar shugabanni irin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a ranar Asabar, 5 ga watan Maris, a jihar Delta, inda ya kai ziyarar ban girma ga Ovie na masarautar Uvwie, HRM Dr. Emmanuel Ekemejewan Sideso; da Olu na Warri, HRM Ògíamɛ̀ Atúwàtse III, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

Irin Buhari ne maganin matsalar tsaro a Najeriya
Sai irin Buhari: Obasanjo ya bayyana wanda iya magance matsalar tsaro a Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Ya kuma kara da cewa gwamnatoci kadan ne suka fuskanci kalubalen tsaro irin wadanda suka dabaibaye Najeriya a halin yanzu kafin Buhari ya hau mulki a 2015.

Kokarin hadin gwiwa da hadin kan sarakunan gargajiya

Yayin da yake jaddada matakai uku da gwamnatin Buhari ta mayar da hankali wajen inganta tattalin arziki, tsaro da yaki da cin hanci da rashawa, Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin na fama da manyan kalubalen tsaro.

Yace:

“A gaskiya, idan aka duba adadi da yawa na wadancan kalubalen tsaro, tabbas ya zama dole a samu shugaba irin Shugaba Buhari da zai iya tunkarar wadannan kalubalen.”

Osinbajo, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin sarakunan gargajiya a fadin kasar nan da kuma gwamnati a dukkan matakai, kamar yadda This Day ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan APC a arewa za su siyawa Umahi fam din takara

Daga karshe, Buhari ya shilla Landan ganin Likita

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari daga karshe ya tashi daga birnin tarayya Abuja inda ya nufi birnin Landan, kasar Birtaniya a yau Lahadi.

Zaku tuna cewa a makon da ya gabata an shirya Shugaban kasan zai tafi Landan daga kasar Kenya bayan halartan taron majalisar dinkin duniya a Nairobi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel