Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta mika kujerar shugaba na ƙasa yankin Arewa ta tsakiya

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta mika kujerar shugaba na ƙasa yankin Arewa ta tsakiya

  • Jam'iyyar APC ta fitar da jadawalin yadda ta kasafta kujerun shugabannin ta na ƙasa yayin da babban taro ke matsowa
  • A jadawalin da ta fitar ranar Laraba, APC ta kai kujerar shugaban jam'iyya na ƙasa yankin arewa ta tsakiya
  • Jam'iyya mai mulki ta saka ranar 26 ga watan Maris, 2022 domin gudanar da babban taro na ƙasa da zata zabi shugabanni

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan, ta fitar da jadawalin rarraba ofisoshin shugabanninta zuwa yanki-yanki yayin da ranar babban gangamin taro na kasa ke kara matsowa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa APC ta zaɓi ranar 26 ga watan Maris ɗin nan da muke ciki a matsayin ranar babban taro na ƙasa, wanda zata zaɓi mambobin kwamitin zartarwa (NWC) na ƙasa.

A jadawalin da APC ta fitar yau Laraba a Abuja, jam'iyyar ta miƙa ofishin shugaban jam'iyya na ƙasa zuwa yankin arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Yadda APC ta karkasa kujerun shugabanci a shiyyoyi 6 na kasar nan

Jam'iyyar APC
Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC Ta mika kujerar shugaba na ƙasa yankin Arewa ta tsakiya Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Matakin kai kujerar shugaban jam'iyya na ƙasa yankin arewa ta tsakiya na nuni da dakatar da yan takarar wani yanki neman shugabancin APC na ƙasa.

Wasu daga cikin yan takarar da hakan zai shafa sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Borno, (Arewa maso gabas) Sanata Ali Modu Sheriff da kuma tsohon gwamnan Zamfara (Arewa maso yamma), Abdul'aziz Yari.

Daily Trust ta tattaro jerin kujerun da Arewa ta tsakiya ta samu kamar haka:

Arewa ta tsakiya

1. Shugaban jam'iyyar na ƙasa

2. Mataimakin shugaban jam'iyya na Arewa ta tsakiya

3. Mataimakin sakataren jam'iyya na ƙasa

3. Mataimakin mai bada shawara kan harkokin shari'a na ƙasa

4. Mataimakin sakataren watsa labarai na ƙasa

Sauran kuma sun ƙunshi mukaman yankin da suka haɗa da, Sakatare, shugaban matasa, sakataren tsare-tsare, shugabar mata, shugaban masu naƙasa da kuma tsaffin shugabanni.

Kara karanta wannan

Kayar Kifi tayi ajalin DIG Egbunike, babban dan sandan dake binciken Abba Kyari

A wani labarin kuma Kwankwaso ya yi babban Kamu, wasu shugabannin PDP sun yi murabus, za su koma NNPP

Wasu kusoshin jam'iyyar PDP a karamar hukumar Rano ta jihar Kano sun yi murabus daga kan mukamansu da nufin bin Kwankwaso.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace zai bar PDP kafin karshen watan Maris, alamu sun nuna zai koma NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel