An tauye 'yancin mata: Matan gwamnonin Najeriya sun fito zanga-zanga a Abuja

An tauye 'yancin mata: Matan gwamnonin Najeriya sun fito zanga-zanga a Abuja

  • A yau Talata ne matan gwamnoni da wasu sanatoci suka fito bakin majalisar dokokin kasar nan domin yin zanga-zanga
  • Suna zanga-zangar ne don nuna kin amincewarsu da yadda majalisa ta yi watsi da wani kudurin mata a kasar
  • An ga matan wasu gwamnoni, musamman na yankin kudu suna bayyana ra'ayoyinsu a wurin zanga-zangar

FCT, Abuja - The Nation ta ruwaito cewa, matan wasu Gwamnonin Najeriya sun bi sahun kungiyoyin mata daban-daban da suka yi zanga-zangar kin jinin rashin adalci kan mata a kofar Majalisar Dokokin kasar a yau Talata.

Wadanda suka shiga zanga-zangar sun hada da matan gwamnan Ekiti Erelu Bisi Fayemi; Edo, Betty Obaseki da Akwa Ibom, Martha Udom.

Matar gwamna Fayemi ne ta jagorance su, inda ta ce sun je filin zanga-zangar ne domin su tsaya wa dukkan matan Najeriya sannan su nuna hadin kansu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige tsohuwar shugabar matan PDP, diyarta da wasu mutum biyu

Majalisa ta shaida fushin matan gwamnoni kan kuduin mata
An taba 'yancin mata: Matan gwamnonin Najeriya sun fito zanga-zanga a Abuja | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

A cewarta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun zo nan ne domin neman hakkinmu. Muna son shugabanninmu a Majalisar Dokoki ta kasa su gane cewa matan Najeriya suna da 'yanci”

Matar gwamna Obaseki kuma da take bayyana goyon bayanta ga zanga-zangar, ta ce duk wanda ya yi watsi da muradin mata zai fadi zabe a jihar Edo.

Matar gwamna Emmanuel, wacce ta jaddada ayyuka 35 na tabbatar da adalci ga mata, ta bukaci a baiwa mata damar su ba da gudummawarsu ga ci gaban al’umma.

Ita ma shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri, ta halarci wajen zanga-zangar.

Ta ce ba wai mata na neman a tausaya musu bane, adalci kawai suke nema.

Wasu Sanatoci mata suma sun shiga zanga-zangar, inda suka yi kira da a samar da daidaito tsakanin maza da mata.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa muka yi bikin zagayowar ranar haihuwar Aisha Buhari a Dubai, Matan Gwamnoni

Tun farko jaridar Punch ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi kira ga mata da su fito domin nuna adawarsu ga yadda aka yi watsi da kudurin mata a majalisar.

Bayan Shan Matsin Lamba Daga Mata, Majalisa Ta Canja Ra'ayinta Kan Dokar Mata, Za Ta Sake Sabon Kuri'a

A wani labarin, Majalisar Wakilai na Tarayya ta canja ra'ayinta game da yin garambawul da sassa uku na kundin tsarin mulki da suke da alaka da 'yancin mata na rike wasu mukamai, rahoton Premium Times.

Hassan Fulata (APC, Jigawa) a ranar Talata ya gabatar da bukatar majalisar da sauya matakin da ta dauka kan wasu kudirori;

Asali: Legit.ng

Online view pixel